…Za Mu Ci Gaba Da Taimakawa Matasa
Daga Imrana Abdullahi
Shugaban Kamfanin sana’ar karafa na “NAK”, Alhaji Akilu Hassan Babaye, ya bayyana cewa nan ba da dadewa ba Kamfanin mulmul karafa na Katsina da ake kira ( Katsina Steel rolling) zai fara aiki.
Akilu Hassan Babaye ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a garin Funtuwa Jim kadan bayan kammala gagarumin taron fadakarwa da wayar da kan matasa game da illa da kuma matsalolin da ke tattere da yin ta’ammali da miyagun kwayoyi.
Akilu Hassan ya ci gaba da cewa sakamakon irin namijin kokari da aiki tukurun da suka shafe tsawon lokaci suna yi, batun kamfanin sarrafa karafa na Katsina zai fara aiki nan ba da jimawa ba.
Akilu Babaye ya kuma yi kira ga daukacin matasa da su kasance masu jajircewa a wajen kokarin inganta harkokin rayuwa ta yadda za su zama abin koyi a cikin al’umma.
” Na kasance abin koyi da kwatancin da a halin yanzu ina da kamfanin da ke dauke da ma’aikta masu digiri na farko da na biyu duk suna aiki a cikin kamfanin da na kafa kuma hakan ya faru ne sakamakon jajircewa da tsayuwa a kan aiki tukuru”.
” Hakika babu abin da nake bukata irin bunkasa tattalin arzikin garin Funtuwa, Jihar Katsina da Najeriya baki don haka ne nake yin dukkan mai yuwuwa domin cimma wannan burin”.
” A kamfanina ina da dimbin jama’ar da na dauka aiki kuma a cikìnsu Kwai masu shaidar karatun digirin farki da na biyu duk suna nan a kamfanin suna gudanar da ayyukansu”.
Sai ya kara da cewa ya kafa makarantar matasa da ake koya masu karatun alkur’ani da sauran al’amuran addinin Islama da aka yi wa matasa a kalla dubu rajista, amma a halin yanzu matasa bai wuce dari Uku (300) ba da suke yin karatu a makarantar ta dare kuma malaman makarantar suna nan har yanzu ana ba su kudin alawus alawus da ake ba su ba tare da an tsaya ba.
” Zan tsayawa matasa masu bukatar yin sana’a a Bankin Ja’iz domin a ba su bashin fara yin sana’a bayan kammala samun horon koyon sana’ar da suke bukata, kuma idan an ba su za su biya bashin ne a shekara daya ta hanyar biyan kudin wata wata”.
Akilu Hassan Babaye wanda shi ne darakta a kamfanin (NAK) ya ci gaba da yin kira ga matasa da su hanzarta kokarin daukar matakan inganta rayuwarsu a kida yaushe ta yadda z a samu wadanda ake cewa manyan gobe.
THESHIELD Garkuwa