Home / Big News / Kasar Saudiyya Ta Tallafawa Marayu Da Ma’aikata

Kasar Saudiyya Ta Tallafawa Marayu Da Ma’aikata

Daga Imrana Abdullahi
Hukumomin kasar Saudi Arabiya sun gargadi Gwamnatin tarayyar Najeriya a game da karatun da aka yi watsi da su cewa za a iya yin amfani da su a cikin sauki wajen aikata ayyukan laifi daban daban.
Wannan gargadi ya fito ne daga bakin wani wakilin da ya wakilci kasar a lokacin wani taron bayar da tallafi domin karfafa gwiwar mutane dubu daya “1000” da suka kasance marayu a kwarai da nufin taimakawa kokarin gwamnatin tarayya na ragewa jama’a radadin talauci da halin kunci da marayu suke ciki a Najeriya.
Da yake jawabi a wajen raba kayan abinci da sauran kayan da za su karfafa wa jama’a gwiwa a Ilorin Babban birnin jihar Kwara, manajan wannan shirin na taimakawa marayu Farid Salman cewa ya yi an tsara wannan shirin ne domin a taimakawa marayu da masu bukata da suka kasance musamman matasa da yara ƙanana, inda ya tabbatar da cewa hakika yin watsi da su wani babban hadari ne a kasa baki daya.
Salman ya kara da bayar da misali da cewa wadanda suka amfana an horas da su a kan sana’o’i daban daban da suka hada da Ɗinki, sana’ar Dafa abinci da kuma fasahar samun bayanai da sadarwa kuma duk an sama masu kayan aikin da ya dace da za su fara da shi ta yadda za su dogara da kansu.
Wadansu da suka jagoranci wadanda suka amfana daga cikin marayun sun bayyana wannan tallafin da cewa yazo a lokacin da ya dace wanda hakan zai taimakawa masu bukatar da suka kasance ƙananan yara.
Sama da mutane dubu daya ne daga cikin Musulmi da wadanda ba Musulmi ba suka amfana da shirin tallafin da nufin dauke ƙananan yara daga kan titi da kuma nesanta su daga ayyukan barna da mugun aiki.

About andiya

Check Also

Cloves farming pilot in Nigeria is significantly gaining Momentum.

By; Imrana Abdullahi Members of the Cloves Producers, Processors, and Marketers Association in Nigeria paid …

Leave a Reply

Your email address will not be published.