Home / Uncategorized / KASUPDA ta kaddamar da takardar shaidar izinin tallace – tallace

KASUPDA ta kaddamar da takardar shaidar izinin tallace – tallace

 

A ranar Laraba 13 Ga watan Nuwamba, shekara ta 2024, Hukumar Tsara Birane da Samar da Ci- gaba ta Jihar Kaduna( KASUPDA), a karkashin jagorancin Babban Darattan, Bldr. Datta Abdurrahman Yahya ta kaddamar da takardar shaidar amincewa da yin tallace-tallace na ababen hawa da sauran nau’o’in abubuwan da ake gudanar da tallace-tallace su, na shekara ta 2025.

Wadan nan ababen hawa da ake gudanar da talla da su, sun hada da: manyan motoci da kanana da babura da kekuna da sauran abubuwan da ake gudanar da tallace-tallace da su kamar su: bar, amalanke da sauransu.

Bayan wadan nan akwai allunan tallace-tallace da ake kafawa da na mannawa a jikin bango da mai amfani da hasken wutar lantarki na zamani da ake da talla da su.

Da ya ke kaddamarwa, a madadin Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, Babban Darattan Hukumar ta KASUPDA, Bldr. Datta Abdurrahman Yahya ya bayyana cewa Jihar Kaduna ita ce Jiha ta biyu da ta riga kaddamar da wannan takardar shaidar gudanar da tallace-tallace.

Ya na mai cewa idan mutum ya karba a Jihar Kaduna ba sai ya sake karba ba a wata Jiha.
A cewar sa, hikimar kaddamarwar da wuri shi ne domin jama’a da kamfanoni su samu damar karba a Jihar kaduna wanda hakan zai sa Jihar ta sami karin kudaden shiga.

Babban Dattan, ya bayyana cewa samar da wannan takarda mai inganci zai taimaka wajan tabbatar da gaskiya da kuma tsabtace wannan aiki da kawar da karbar ta bogi.

A jawabansu daban-daba, Hukumomin Gwamnati da kamfanonin tuntuba da wakilai daban-daban da suke gudanar da wannan aikin bayar da wannan takardar shaida sun yabawa Babban Darattan bisa kyawawan manufofin shi na tabbatar da gaskiya da adalci, sa’annan suka tabbatar da bayar da goyan-bayan su da hadin kai domin samun nasaran shirin.

Nuhu Garba Dan’ayamaka, MNIPR (Mataimakin Darattan yada labarai)

Hukumar Tsara Birane da Samar da
Ci-gaba ta Jihar Kaduna(KASUPDA).
14 Ga Watan Nuwamba, 2024

About andiya

Check Also

Shugaban Matasan PDP Na Shiyyar Arewa Maso Yamma Ya Yaba Tare Da Yi Wa Husaini Jalo Jinjinar Bangirma

  Shugaban matasa na jam’iyyar PDP na shiyyar Arewa maso Yamma Alhaji Atiku Muhammad Yabo, …

Leave a Reply

Your email address will not be published.