Related Articles
Imrana Abdullahi
Daukacin al’ummar Jihar Katsinawa tun daga kan Gwamnan Jihar Katsina Aminu Bello Masari, tare da mataimakinsa Mannir Yakubu da Sarkin Katsina da duk wani mai fada aji daga manyan ma’aikatan Jihar Katsina, yan kasuwa da shugabanni suna tururuwa a gidan Malam Danjuma Katsina domin yi masa ta’aziyyar rasuwar Mahaifiyarsa da Allah ya yi mata rasuwa bayan fama da rashin lafiya.
Hakika Tururuwar manyan mutanen da Allah ya ba jagorancin Jihar Katsina a hannunsu ya bayyana karara irin daraja da martabar da Allah madaukakin Sarki ya yi wa Malam Danjuma Katsina.
Kuma kamar yadda masu iya magana ke cewa kamannun duniya sune na kiyama wato dukkan wanda Allah ya yi wa jama’a ya bashi arzikin da zai zama abin sha’awa ga kowa.
A ingantattun bayanan da muka samu sun tabbatar mana cewa hatta Gwamnan Jihar Katsina tare da mataimakinsa da kuma Sarkin Katsina duk sun yi wa Malam Danjuma waya suka yi masa ta’aziyya wanda ba dukkan mutum kan samu irin wannan alfarmar ba.
Ga kuma manyan yayan Jihar Katsina da suka hada da manyan ma’aikatan Bankuna,Yan kasuwa da kusoshin Gwamnati tun daga kan yan majalisar zartaswar Gwamnatin Jihar Katsina da shugabannin hukumomin Gwamnati da dimbin Daraktoci, manyan yan siyasa da wadanda Dabensu yaji makuba duk sun halarci gidan shahararren Dan jarida Malam Danjuma Katsina domin yi masa ta’aziyyar rasuwar mahaifiyarsa.
Faruwar hakan dai ya bayyana a fili irin yadda Malam Danjuma Katsina yake zaune da kowa lafiya