Home / Uncategorized / Kotu Ta Rushe Zaben Adamu Usman Mr La A Kaduna

Kotu Ta Rushe Zaben Adamu Usman Mr La A Kaduna

Babbar kotun Gwamnatin Tarayya da ke zamanta a Kadunata rushe zaben dan takarar majalisar Dattawa Adamu Usman da ake wa lakabi da (Mr La) na jam’iyyar PDP.

Indai za a iya tunawa a kwanan baya ne Honarabul Usman Ibrahim Sardainan Badarawa ta hannun lauyansa babban lauyan Najeriya Samuel Atung ya shigar da karar korafin cewa an yi masu aringizon kuri’u lokacin da aka yi zaben fitar da dan takarar kujerar Sanatan Kaduna ta tsakiya a karkashin jam’iyya PDP.

Alkalin babbar kotun Gwamnatin tarayya da ke zama a Kaduna Alkali Muhammad Garba Umar, ya ce kotu ta Gamsu da irin hujjojin da mai kara Honarabul Usman Ibrahim ta hannun lauyansa Samuel suka gabatarwa da kotu a game da korafin yin aringizon kuri’a lokacin da aka gabatar da zaben fitar da Gwamnin domin samun wanda zai tsayawa PDP takarar Sanata a mazabar Kaduna ta tsakiya.

Lauya Samuel da Honarabul Usman Ibrahim duk sun shaidawa manema labarai cewa daman kotu ce kawai ta ragewa masu karamin karfi a duk lokacin da suke da wata matsala makamanciyar hakan, kuma suna godiya ga jama’a da suke ba su hadin kai da goyon baya.

 

Mai shari’a Muhammad Garba Umar ya ce hakika dukkan hujjojin da mai kara ya gabatar da kuma irin kokarin da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta yi na ta sake sabon zabe duk suna kan ka’ida kuma kotu ta Gamsu da hakan don haka kotun ta rushe zaben ta kuma bayar da umarnin a sake sabon zabe nan da kwanaki sha hudu (14) masu zuwa.

About andiya

Check Also

Remain steadfast against security challenges” – CDS General Musa to army officers and men

  The Chief of Defence Staff , General Christopher Musa has tasked the Nigeria Army …

Leave a Reply

Your email address will not be published.