…sun fara shirye shiryen sake zaben Uba Sani da Bola Ahmed Tinubu
Daga Imrana Abdullahi
A kokarin da Kungiyar APC Ciki Da Waje keyi na ganin an sake zaben Gwamna Sanata Uba Sani da kuma shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu a yau ranar Talata 17 ga watan Maris, 2026 kungiyar ta kira daukacin kodinetocinta da ke garin jihar Kaduna da kuma shugabannin a matakin Jiha karkashin jagorancin Alhaji Musa Bawa FCNA, inda suka yi masu rabon Shinkafa da Kudi tare da ba su hakuri kasancewar ana tare wajen fafutukar ganin an sake samun nasarar lashe zabe a shekarar 2027.

Shugaban kungiyar APC Ciki Da Waje Alhaji Musa Bawa FCNA, ya bayyana cewa lallai kungiyar APC Ciki da Waje a koda yaushe ya na kokarin ganin yin aiki ne domin ganin Gwamna Uba Sani da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu sun sake lashe zabe a shekarar 2027 mai zuwa da ikon Allah.
” Akwai ayyukan raya kasa tari da yawa da Gwamnatin Uba Sani ke shimfidawa a dukkan wuraren birane da karkara da suka hada da ayyukan Hanyoyi, aikin asibiti,ayyukan bunkasa ilimi,da kuma bunkasa Noma da sauran ayyukan raya kasa da ci gaban al’umma daban daban.
Honarabul Ado Dogo Audu babban mai ba Gwamna Uba Sani Shawara, ina tare da wannan ƙungiya ne domin na san irin kokarin da kungiyar Ciki da waje suke yi a koda yaushe.
“Ayi ta hakuri a kuma ba shugabancin Alhaji Musa Bawa cikakken hadin kai da goyon baya domin nasara na nan tafe da yardar Allah, kun ga idan an samu nasara duk abin da aka na Kungiyar APC Ciki Da Waje ne, a cikin ku ne shugaban zai zabo ko ya ce a kawo mutune guda Kaza domin a ba su duk muƙamin da aka ba wannan ƙungiya, haka kuma idan aiki ne duk haka za a raba abin a cikin yaya kungiyar”.
Don haka muke yin kira ga dukkan jama’a da jagororin wannan ƙungiya da su kara daura dammarar gudanar da aiki tun daga masani zuwa matakin kananan hukumomi da Jihar Kaduna baki daya.

Da akwai kungiyoyin da suke taimakawa Gwamnati da yawa amma sai kawai su zo wurin gwamnati suna neman wani abu amma wannan ƙungiya ta Ciki da Waje ta na kokarin yin ayyuka ne da kanta wanda ita ta san inda take samun kudin da take yin abubuwan da take yi
Idan an samu kamar wannan ƙungiya guda Goma sai dai mu koma gida muyi bacci kawai domin za a samu nasarar da ake bukatar a samu

Wani daga cikin jagororin kungiyar APC Ciki Da Waje daga garin Zariya ya bayyana dalilin da suka sa suke kokarin goyon bayan tafiyar Gwamnatin jihar Kaduna karkashin Gwamna Uba Sani, wanda kadan daga cikin dalilan sun hada da samun Takin Zamani da kuma samar da katafaren ofishin kungiya mai kyau a garin Zariya da kowa ne dan jam’iyya ke alfahari ya na kuma yin amfani da shi wajen yin tarurruka.
THESHIELD Garkuwa