Daga Imrana Abdullahi
Kungiyar matasan arewacin Najeriya karkashin jagorancin Arewa Youth For Liberty (AYFL) sun bayyana Nagarta, aiki tukuru da son jama’a tare da kokarin rikon gaskiya da yin adalci a matsayin abin da ya ja hankalinsu wajen tunanin bayar da karramawa ga tsohon Alkali mai ritaya Honarabul Ibrahim Buba, Walin Mambila kuma Turakin Gashaka.
A ranar Asabar ne 5 ga watan Agusta, 2023 matasan na Arewa suka Karrama Alkali Ibrahim Buba da lambar Yabo ta “Majidadin Matasan Arewa”.
Jim kadan bayan karbar karramawar da kuma gabatar da wani kwarya kwaryan jawabi ga mahalarta taron.
Alkali mai Murabus Ibrahim Buba ya shaidawa manema labarai cewa ya ji dadi kwarai da aka lalubo shi a cikin jama’a domin wannan karramawa, musamman da matasa suka yi masa.
“A lokacin da muke yara ana gaya mana cewa matasa ne shugabannin gobe don haka ni tawa goben ta zo kenan, saboda daga an yi maganar gobe kawai ana jiran lokaci ne kawai sai dai abin da zaka yi da lokacin da kake da shi ya na da matukar amfani kwarai don haka ne muke yin kira ga matasa kada su yi wasa da lokacin su domin lokaci ne da ya dace aje makaranta lokaci ne da ya dace har aje jami’a ma don haka ya dace su kasance a cikin aikata wadansu abubuwan da suke da amfani a rayuwarsu da kasa baki daya”.
Saboda haka idan sun je makaranta lallai ne su kasance suna neman ilimi mai kyau kuma mai inganci saboda da an ba su takardar shedar kammala karatu su kasance za su iya kare takardar da aka ba su a koda yaushe
Hakika a yau ina matukar farin ciki kwarai da karramawar da Matasan Arewa suka yi Mani a karkashin Arewa Youth For Liberty (AYFL) suka yi mani”.
“Idan mutum ya na matashi hakika akwai wadataccen lokaci don haka ya dace ya Sani cewa sune za a dogara da su wata rana a matsayin manyan gobe musamman wajen ginin kasa. A yau a kasar Indiya ana takama da ci gaban matasa, don haka kada don kana matashi ko matasa suje can karkashin inuwar su yi ta Bacci kana kallon masu yawan shekaru suna yin aiki, saboda haka idan har mutum ya rasa samun ilimi lallai ka rasa damarka a matsayin matashi”.
“Wato abin da nake cewa shi ne kowane Uba ya na da aikin da ya hau kansa na tabbatarwa batun tarbiyya ya fara daga gida domin daga nan ne ake fara yin tarbiyyar ginin al’umma idan ko mutum ya samar da yara marasa tarbiyya lallai ya ba ta al’umma don haka kada mutum ya samu yayan da ba zai iya kai su makaranta ba dole ne mutum ya haifi yayan da zai yi wa tarbiyya ya kuma ba su ilimi. Kun ga wasu mutane na kallon cewa ilimi wani abu ne kawai ka samu takardar shaidar kammala karatu, a’a ya na fara wa ne daga gida shi ne ilimi, idan da kowa na yin aikin da ya dace ya yi da ba za a samu batun cin hanci da rashawa ba a cikin al’umma”.
Sai kawai mutum ya yi zamansa a guda ya na kallon dansa na amfani da babbar wayar salular da kudin ta ya kai naira miliyan daya, amma kawai mutum sai ya rika kallon yarsa ko dansa ba tare da ya tambaye shi yadda ya samu wannan wayar hannun ba don haka kai ma da kanka ka gurbace da batun rashawa domin ba tayar da iyaye za su bari yayansu na yin bukatar da ta wuce samun su kuma a irin wannan rayuwarce mutum zai rika tuhuma r jami’an Gwamnati yadda suke rayuwa ko gudanar da ayyukansu”.
“Mu yi yaki da cin hanci da rashawa tun daga cikin gidajen mu sai mu ci nasarar Yakin a gari ko kasa baki daya. Ta yaya za a ce matasa da karfe Goma suna kwance a kan gadonsu kawai tare da wayoyinsu amma iyayensu na ta fama da aiki a guda na Dafa abinci yin share share da wanke wanken kayayyakin abinci da sauransu, kai ni ba zan amince da hakan ba a cikin gida na. Abin da nake yi zan gaya maka ba ko Kwabo ni idan na tashi da safe a cikin gida na idan ban ga yaro na yazo gaishe ni ba to ni zan je in gaida su domin zan ke dakinsu in ce na zo in gaishe ku ne. Amma akwai wasu mutanen da z su yi tsawon kwanaki uku ba su sa yayansu a ido ba amma sai su rika kalubalantar duk wani abin da Gwamnati za ta tafiyar”, inji Ibrahim Buba.