Home / Labarai / Kungiyar Mawallafa Da Marubuta Ta Arewa Publishers Forum Ta Karrama Shugaban Gidauniyar Zakka Da Wakafi

Kungiyar Mawallafa Da Marubuta Ta Arewa Publishers Forum Ta Karrama Shugaban Gidauniyar Zakka Da Wakafi

Daga Imrana Abdullahi Kaduna, Arewacin tarayyar Najeriya

A satin da ya gabata ne kungiyar Marubuta da Mawallafa ta Arewacin Najeriya wato (Arewa Publishers Forum) ta karrama shugaban gidauniyar Zakaat  and Waqaf ta jihar Kaduna ƙarƙashin jagorancin Abdullahi Salisu Halidu da lambar girmamawa bisa abubuwan alkhairi da yake yi na taimakawa marayu da marasa galihu a cikin al’umma a garin Kaduna da kewaye.

Yayin da yake mika masa lambar yabon Sakataren ƙungiyar Malam Idris ya godewa Abdullahi Salihu kan irin taimako da gudumawar da yake bai wa addini ta fuskar taimakawa marasa ƙarfi da marayu a cikin al’umma.

Jim kaɗan bayan amsar lambar yabon, shugaban gidauniyar Abdullahi Salisu Halidu ya nuna farin cikinsa da godiya ga Allah SWT da ya nuna mishi irin wannan rana wanda ƙungiyar suka ga ya cancanta da su karrama  shi da lambar girmamawa,ba don komai ba sai don wasu ayyuka da suka ce yanayi wanda ba yinsa bane.

“Na kan gaya wa jama’a da yawa ba yi na bane, Allah (SWT) shi ya ke zaɓan wanda zai ba wakilci da irin wannan jagoranci.” In ji shi.

Yana mai cewa, haƙiƙanin gaskiya wannan gidauniya shi ya assasata: “amma ko da na assasata ban so jagorancinta ba, na yi na yi in sami wani wanda zai yi jagorance ta ,amma wanda muke tare suka nuna lalle ni suke so in jagoranceta, cikin ikon Allah, Allah ya ƙudurta hakan. Ya kuma bamu ikon gudanar da jagorancin har zuwa yanzu”, in ji shi.

“Irin wannan abin da kuka yi mana shi ke ƙarfafamu, shi ke zaburar da mu da ke nuna mana cewa muna kan turba ta gaskiya muna yin abin da ya dace. To Alhamdulillah”, a cewarsa.

Ya kuma ƙara da cewa, abu na biyu da ya ƙara bani sha’awa da  ƙarfin guiwa shi ne yanzu zamani ya kai duk abin da kake yi la’alla siyasa, ko taimaka wa addini ne, ko kasuwanci ko wane fanni na rayuwa, wannan abin naka ba zai sami ɗaukaka ba sai  an haɗa da masu sana’a irin naku wato kafafen yaɗa labarai. To Alhamdulillah,wannan nasara ce gare mu baki daya.

Har wala yau, shugaban gidauniyar ya bayyana cewa, kullum ina gayawa mutane cewa, Allah da ya halicce mu shi ya tsara mana sadaqah, zakkah,waqaf amma mun bar Yahudawa wasu can da ban suka cire mana wannan daga fannin rayuwar mu suka sanya mana haraji.

“Wallahi sakamakon haka shi ne muke samun taɓarbarewar rayuwa, tsananin talauci har da taɓarbarewar tsaro, duk wannan shi ne dalili”, Ya ce.

A cewarsa, a ko yaushe ina maganar Zakkah da Waqaf sai na bada misalai da wasu ƙasashe da suke nan kusa damu ko da suke nesa damu.

Kazalika, ya ce mu kan gayawa gwamnati, masu hannu da shuni, mu saki dukkan wannan hanya mu koma kan Zakkah da Waqaf ita ce mafita a rayuwarmu.

Daga ƙarshe ya ce a  madadin shi da membobin gidauniyar Zakkah da Waqaf muna ƙara mika godiyar mu kuma muna miƙa hannun mu na haɗaka da ku wajen gudanar da aikace aikacen mu

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.