Home / Labarai / Kungiyar NUJ Reshen Arewacin Nijeriya Ta Dage Taron Da Ta Shirya

Kungiyar NUJ Reshen Arewacin Nijeriya Ta Dage Taron Da Ta Shirya

Imrana Abdullahi

Kungiyar yan jarida reshen arewacin Nijeriya ta Yamma ta bayar da sanarwar dage wani babban taron tattaunawar da ta shirya yi a dakin taro na gidan Tunawa da Sardauna da ake kira gidan Arewa cikin garin kaduna.

Tun da farko dai kungiyar reshen Arewa ta Yamma Yamma shirya gudanar da wannan taro ne a ranar Asabar 21, ha watan Maris, 2020.

Kamar yadda reshen arewacin Nijeriya ta Yamma na kungiyar ya bayyana cewa dage taron ya zamo wajibi sakamakon irin duba da yadda batun cutar Korona birus ke girgiza duniya kuma har Gwamnati ta dauke wadansu tarurruka da ta shirya a matakai daban daban.

A cikin wata takardar sanarwar da ta fitar mai dauke da sa hannun mataimakin shugaban kungiyar na kasa reshen arewacin Nijeriya Kwamared Yusuf Idris da kuma shugaban kungiyar reshen Jihar kaduna kwamared Adamu Yusuf, Bali daya sun bayyana cewa daukar matakin ya biyo bayan irin matakin da kungiyar Gwamnonin arewacin kasar suka dauka ne a taron da suka yi da kuma wadansu hukumomi da dama da nufin hana cutar yin tasiri baki daya a kasar  don haka ne kungiyar ta bayar da cikakken hadin kai da goyon bayan ta bisa wannan matakin.

Kungiyar ta yi kira ga daukacin yan Nijeriya Nijeriya su bayar da cikakken hadin kansu da goyon baya game da matakan da Gwamnatin ke dauka na hana yaduwar wannan cuta a cikin jama’a.

Kungiyar ta tabbatar da cewa nan gaba kadan da an samu ingantawar al’amura za a gudanar da wannan taron na tattaunawa na Yammacin kasar da kungiyar Yan Jarida suka shirya.

Kungiyar ta kuma yi godiya fa muhimman mutanen da suka shirya zuwa taron domin gabatar da kasidu da sauran muhimman bayanan da za su taimaki kasa da al’ummarta baki daya, ta bayyana su a matsayin yan kishin kasarsu sin taimakawa kasa tare da Jama’arta a samu dukkan nasarorin da kowa ke fatan samu.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.