Related Articles
Daga Imrana Abdullahi
Tun bayan samun fafatawar da kulab din kwallon kafa guda 17 suka yi domin cin kofin tunawa da KOSI Madukwe a filin wasa na gidan rediyon Hamada wanda Abdallah Yusuf Mamman ya Sanya domin taimakawa matasa masu jiki a Jika da ke tasowa kuma suna sha’awar yin wasan kwallon kafa.
JKD Academy dai ta samu nasara ne a kan kulab din wasan kwallon kafa na Young Pillars a wasan karshen da suka buga a filin wasan kwallon kafa na dandalin Murtala da ke cikin garin Kaduna.
Kulab din guda biyu dai sun fafata ne a neman zama zakaran gasar KOSI Madukwe wanda Abdallah Yusuf Mamman ya Sanya masu kofin gasar domin tunawa da abokinsa da ya rasu kuma an fara buga wannan kofin ne karo na farko kamar yadda wanda ya Sanya.
Kamar yadda muka samu labari daga wanda ya Sanya kofin Abdullah Yusuf Mamman ya ce kulab din wasan kwallon kafa na yan kasa da shekaru 15 an samu kulab guda 17 da suka fafata a gasar, amma bayan fafatawa a tsakanin su sai aka samu kulab guda biyu da suka samu zuwa gasar karshe da kulab din JKD Academy da Young Pillars suka fafata a wasan karshe kuma bayan bugun daga kai sai mai tsaron gida sai nasara ta tabbata ga Kulab din JKD Academy da ke Kaduna.
Wasan karshen dai da aka fafata a filin wasa na dandalin Murtala da ke Kaduna ya samu halartar tsofaffin yan wasan kwallon kafa da suka yi suna a Najeriya da suka fito daga Kaduna a arewacin kasar da suka hada da Dahiru Sadi, Ali Nayara da sauran muhimman mutane masana wasan kwallon kafa kamar Mohammad Sani shugaban alkalan wasa na Jihar Kaduna da yan uwan Abdallah Yusuf Mamman Maza da Mata da dai sauransu.
Da yake tofa albarkacin bakinsa tsohon dan wasan kwallon kafa Ali Nayara bayyana farin cikinsa ya yi da irin yadda ya ga yaran na wasa abin da ya bayyana da cewa za a samu masu zuwa gobe a harkar kwallon kafa a nan gaba.
Sai dai Ali Nayara ya yi kira ga Gwamnatin Jihar Kaduna da ta samar da gagarumin kulab din wasan kwallon kafa na Jihar ta yadda kowa zai yi alfahari da shi musamman a tsakanin matasa.
Da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala gasar wanda ya Sanya kofin da aka fafata Abdallah Yusuf Mamman alkawari ya yi na cewa zai ci gaba da Sanya kofuna domin matasa da dama su fafata a nan gaba.
Abdallah ya ci gaba d bayanin cewa ya na yin kira ga daukacin al’umma da su rika taimakawa matasan da suke wasan kwallo ta yadda idan Allah ya Sanya a nan ne hanyar cin abincin matashi yake to sai kawai nasarar ta tabbata ga tare da samun tangarda ba.
Ya kuma yi godiya ga daukacin manyan bakin da suka halarci gasar da suka bayar da gudunmawa ta yadda yaran da ke wasan Kona nan gaba za su so zama kamar wadanda suka yi wasan a can baya da duniya ta san da zamansu a halin yanzu.
Kowane kulab dai sun samu shahadar da ke nuni da cewa sun halarci gasar
Sannan kuma dukkan kulab din da ya zama na daya da na biyu duk sun karbi kyautar makudan kudi naira dubu Hamsin Hamsin domin karfafa masu Gwiwa.