Home / Uncategorized / Kungiyoyi Dubu Sittin Da Biyar Na Fafutukar Lashe Zaben Tinubu A 2027 – Galadiman Takai

Kungiyoyi Dubu Sittin Da Biyar Na Fafutukar Lashe Zaben Tinubu A 2027 – Galadiman Takai

 

Daga Imrana Abdullahi
Shugaban Kungiyar gamayyar matasan arewa, Abubakar Aliyu Galadiman Takai ya bayyana cewa babban burin da suka sanya a gaba shi ne ganin shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sake samun gagarumar nasara a zabe shekarar 2027 mai zuwa.

A wani taron manema labarai da ya kira a Kaduna Shugaban gamayyar kungiyoyin matasan Abubakar Aliyu Galadiman Takai ya shaidawa manema labaran cewa babban dalilinsu na goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu shi ne domin suna bukatar ci gaban arewacin kasar ne ta fuskar irin ayyukan ci gaban yankin da aka fara a can baya amma kuma sai ayyukan suka tsaya haka kawai.

“Don haka ne muka yi iyakar kokarin mu domin ganin an dawo ci gaba da aiwatar da wadannan ayyukan, hakan ya sa muka rubutawa shugaban kasa muna rokonsa da mu matasa muna so a dawo da wadannan ayyukan kamar aikin samar da Titi daga Kaduna zuwa Abuja,aikin samar da wadatacce kum isasshiyar Iskar Gas da zai taimakawa yankin arewa da kasa baki daya ta fuskar samar da ingantaccen tattalin arzikin kasa sai kuma aikin samar da Mai fetir da aka fara a jihar Bauchi na Kwalmani da kuma aikin jawo ruwan Teku zuwa tashar baro da dai ayyuka da dama duk kuma shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da hakan wanda ba karamin ci gaban yankin ab nr da kasa baki daya”, inji shugaban matasa.

” Ba ta yadda za a iya samun ci gaban yanki,kasa ko nahiya a halin adawa da Gwamnati don haka muke kokarin ganin Gwamnatin Tinubu ta samu nasara ta yadda kowa jama’ar kasa za su samu ci gaban da kowa ke bukata,fatan mu da burin mu kenan”.

Galadiman Takai ya ci gaba da bayanin cewa a cikin gamayyar kungiyar ta su akwai zunzurutun kungiyoyi sama da dubu Sittin da biyar (65,000)da suke  cikin wannan gamayyar kuma dukkansu kowa na kokarin ganin an samu nasarar lashe zaben shugaba Bola Ahmed Tinubu ta yadda za a ci gaba da saita kasa a samu nasara mai dorewa.

“Gamayyar kungiyoyi dubu sittin da biyar da suka kasance daga arewacin Najeriya jihohi Goma sha Tara duk sun yi nisa wajen ganin haka ta cimma ruwa Tinubu ya sake lashe zabe a shekarar 2027 mai zuwa da yardar Allah.

Galadiman ya kara da cewa a cikin lokacin Azumin nan an ga irin yadda matar shugaban kasa Sanata Remi Bola Tinubu take ta zuwa daga waccan jiha zuwa waccan ta na rabon kayan arziki da kuma ayyukan kula da lafiyar jama’a a jihohin arewacin Najeriya saboda haka muke yabawa da irin wannan kokari na uwar gidan shugaban kasa.

“Wannan gamayyar kungiyoyi dubu sittin da biyar za ta bude wadansu ofisoshin shiyya a jihohin Bauchi da Nasarawa da kuma Kaduna wanda daman akwai shi tun da dadewa, duk domin kara karfafa wannan tafiya ta samun nasarar shugaba Bola Ahmed Tinubu”.

About andiya

Check Also

Senator Yar’adua Hands Over MCHC Tsakatsa

By Lawal Gwanda A befitting Maternal and Child Health Centre constructed by Senator AbdulAziz Musa …

Leave a Reply

Your email address will not be published.