Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya bayyana Kwalejin Ilimi ta Tarayya ta ƙere-ƙere da ke jihar a matsayin wani ginshiƙin samar da ƙwararrun malamai a makarantun gwamnati a Zamfara.
Majalisar Gudanarwa ta Kwalejin Ilimi ta Tarayya (Technical) da ke Gusau, ta kai wa Gwamna Lawal ziyarar ban-girma a gidan gwamnatin Jihar Zamfara da ke Gusau a ranar Laraba.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta bayyana cewa, sun kai ziyarar ban-girma ne domin fahimtar juna da kuma inganta haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin jihar da majalisar FCET ta Gusau.
A nasa jawabin, Gwamna Lawal ya yi maraba da mambobin majalisar gudanarwar tare da jaddada buƙatar bai wa Kwalejin Ilimi ta Tarayya duk kulawar da ta dace.
“Ina so in fara da cewa al’ummar Jihar Zamfara sun daɗe su na cin gajiyar Kwalejin Ilimi ta Tarayya, Gusua. In ma taƙaice zance: ‘yan uwana mata kusan biyar ne suka yi karatu a FCET.
“Kamar yadda shugaban ya bayyana, a fannin ilimi, Jihar Zamfara ta kasance a baya tsawon shekaru. Gogayya mu ke yi da Yobe a matsayi na ƙarshe.
“A shekarar da ta gabata, na kafa dokar ta-ɓaci a ɓangaren ilimi na Zamfara saboda ƙalubalen da ake fuskanta a fannin. Abin takaici, a cikin shekaru uku da suka gabata, gwamnatin da ta shuɗe ta kasa biyan kuɗin jarrabawar NECO da WAEC na ɗalibai. Duk da haka, mun biya bashin, wanda yanzu ya zama tarihi.
“Kwanan nan, mai yiwuwa ka karanta a labarai game da ƙwazon da ɗalibanmu suka yi a jarrabawar ɗalibai maau hazaƙa na NECO. Jihar mu ta Zamfara ta zama jihar da ta zarra a duk faɗin Arewa kuma ta biyu a faɗin ƙasar nan.
“Mun himmatu wajen ganin kowane yaro ya samu ingantaccen ilimi. A yanzu haka muna gyara da gina makarantu sama da 290 a faɗin jihar nan.
“Matakan da muke ɗauka sun haɗa da samar da ingantattun kayan karatu da kuma ba da horo ga malaman mu. A cikin wannan yunƙurin, FCET tana taka rawar gani yayin da muke son haɓaka iyawa da ingancin malaman mu. Don haka za mu yi aiki kafafa-da-kafaɗa domin gyara harkar ilimi a Jihar Zamfara.
Tun da farko, Farfesa Muhammad Bashir Nuhu, shugaban majalisar gudanarwa na Kwalejin Ilimi ta Tarayya (Technical), ya yaba wa gwamnan bisa ba da fifiko ga ilimi a cikin ajandar gwamnatinsa.
Ya ce, “Mu ne majalisar gudanarwar babbar kwalejin FCET. Ana ɗaukarta da daraja domin ita kafai ce irinta a faɗin tarayyar ƙasar a lokacin da aka kafa ta. Lokacin da aka kafa ta, an yi ta hassada da yawa game da dalilin da ya sa aka kafa ta a Zamfara. Daga baya na gane cewa wannan ya faru ne saboda jihar Zamfara na ɗaya daga cikin jihohin da suka fi fama da matsalar ilimi.
“A yau, mun zo nan ne saboda gwamnatin ku ta ayyana dokar ta-ɓaci a fannin ilimi na jihar da kuma kyawawan matakan da kuke ɗauka na inganta fannin.
“Muna yaba muku da ƙoƙarinku, kuma muna so mu yi amfani da wannan dama wajen yaba wa uwargidan gwamna Hajiya Huriyya Dauda, wadda ta ɗauki nauyin ɗalibai 20 a ƙwalejin tare da bai wa ɗalibai uku na farko da suka yaye na’ura mai kwakwalwa guda uku.”