ZIYARAN NEMAN ALBARKA IYAYEN KASA
maigirma shugaban kungiyar kwallon kafa mallakin jihar Bauchi Wikki tourist FC Alh Balarabe Douglass tare da sauran Yan majalisun sa da Kuma Yan Wasa suka Kai ziyara domin neman albarka wa maimartaba sarkin Bauchi Alh Dokta Rulwanu Sulaiman Adama.
A nasa jawabin shugaban kungiyar kwallon kafa mallakin jihar Bauchi Alhaji Balarabe Douglas ya bayyana cewa kungiyar ta kawo ziyara ne domin neman albarka iyayen kasa da Kuma addu’ar samun nasara a wasan da za su Fara Bugawa na shekarar 2021/2022.
Maigirma Shugaban kungiyar kwallon kafa mallakin jihar Bauchi Alhaji Balarabe Yusuf Muktar ya Kara da cewa maigirma Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Mahammed Kauran Bauchi ya ba da dukkan wani goyan baya da abubuwa da suke nema domin na shiga kakar wasan da za’a fafata na shekara ta 2021/ 2022.
Maimartaba sarkin Bauchi Alh Dokta Rulwanu Sulaiman Adamu, ya nuna farin ciki da godiya ga shugaban kungiyar na wikki tourist a bisa wannan tunani da ya yi da Kuma godiya matuka a gare shi.
Maimartaba sarkin Bauchi Alh Dokta Rulwanu Sulaiman Adamu ya yi ma wanna kungiya ta wikki touris addu’ar samun nasara da Kuma kariya a dukkan wani Wasa da za ta buga tun daga gida Bauchi har zuwa makwabatan ta.
Maimartaba sarkin Bauchi Alh Dokta Rulwanu Sulaiman Adamu ya Kara yabawa maigirma gwamnan jihar Bauchi Sen Bala Mahammed Kauran Bauchi a bisa yadda yake kokarin tabbatar da kowani irin nasara a jihar Bauchi ta fannoni daban da ban
Maimartaba sarkin Bauchi Alh Dokta Rulwanu Sulaiman Adama yayi musu fatan alheri da Kuma addu’ar samun albarka na jinin Babu yakubun Bauchi.
Allah ya nada kowa lafiya ya saka wa maigirma shugaban kungiyar kwallon kafa mallakin jihar Bauchi Alh Balarabe Yusuf Muktar da mafificin alheri ya kuma Masa jagoranci a dukkan wani mataki ameen ya Allah
Jamilu Barau Daga Bauchi