Home / Uncategorized / Kwamitin Mauludi Da Qafilatul Mahabbah Sun Tallafawa Majinyata 200 A Funtuwa

Kwamitin Mauludi Da Qafilatul Mahabbah Sun Tallafawa Majinyata 200 A Funtuwa

Daga Wakilin mu
Bayanan da muke samu daga Funtuwa a cikin karamar hukumar Funtuwa Jihar Katsina arewacin tarayyar Najeriya na cewa  Kwamitin Zagayen Maulud haɗin gwuiwar Qafilatul Mahabbah Sun tallafawa  Majinya 200 a Asibitin Funtua
 Kwamitin Zagayen Maulidi na Karamar Hukumar Funtuwa hadin gyiwa da Qafilatul Mahabbah reshen Funtuwa,sun bada tallafi kudi da a bincin ga majinyata 200 da ke Kwance a Babban Asibitin Funtuwa .
Shugaban Kwamitin Zagayen gayan Maulidin,Malam Bashir Muhammad Kin Da Shugaban Kungiyar Qafilatul Mahabbah Barista , Ahmad Tijani Magaji Funtua sun bayyana cewa,sun shirya wannnan ziyarar ne ga wadanda Allah ya jarabta da rashi lafiya domin jajanta masu da kuma ba su tallafin kudi da Abinci albarkacin murnar haihuwar Manzan Allah (SAW) .
Bayan Zagayen Maulidi da kuma na zaune da mukeyi sai kuma wannan ziyara ta marasa lafiya Asibitici da Gidan Gyarahanki duk Muna kai ziyarar Maulidi ga ‘yan Uwa mu da suka gamu da jarabawar .
Shima Ansa jawabin Babban Limamin Masallacin Juma’a na Funtuwa Liman Abudurahamman Jibril ya Jagorancin malamai wajan yin nasiha ga majinyatan da masu jinyar su.
  Liman da sauran Malamai Wanda suka haka da Malam Ahidu Shugaban Kadiriya na Funtuwa da Malam Yusif Lawandi da Khilfa Shehu Halilu Dandume da Dr Kabir Shehu Rufai Bakori ne suka Jagorancin bada tallafin da kuma yin nasiha ga majinyatan.
 Darakta DNC Abdullahi D Umar, ya bayyana godiyar su a madadin Hukumar gudanarwa Asibitin a kan wannan tallafin da aka ba masara lafiya da ke Kwance a Asibitin.
DNC Umar ya kuma tabbatar da cewa wannan tallafin zai taimaka masu sosai, tallafin ya hada da kudi da Abinci.
Daraktan ya Kuma jinjina wa gamayyar Kungoyiyi da suka bayar da  wannnan tallafin albarkacin haihuwar Manzan Allah SAW.

About andiya

Check Also

10,000 South East Pupils Get School Bags From Collins Onyeaji Foundation

    No fewer than 10,000 pupils in the South East Zone of Nigeria are …

Leave a Reply

Your email address will not be published.