Daga Imrana Abdullahi
Gamayyar Kungiyoyin Arewa 593 daga jihohi 19 na Arewacin Nijeriya ( AREWA CONSENSUS MOVEMENT) sun bayyana cewa lokaci ya yi da za’a kawo karshen matsalar musgunawa Fulani Makiyaya a fadin kasar nan.
Shugaban Gamayyar Kungiyoyin na Kasa Dakta Awwal Abdullahi Aliyu, shine ya bayyana haka Jim kadan bayan kammala wani taron kungiyar tayi da kungiyoyin Fulani da wasu kungiyoyi daga fadin Nijeriya wanda ya gudana a jihar Kaduna.
Shugaban ya ce Kungiyarsu ta himmatu wajen tabbatar da cewa an daina musgunawa Fulani, inda ya ce suma mutane ne ‘Yan kasa kamar kowa da kuma sauran ‘Yan Arewa da suke rayuwa a Arewacin Nijeriya dama kudan kasar .
” Mun gudanar da wannan taro ne domin tattauna matsalolin mutananmu daga Arewa da kuma ‘Yan Arewa da ke zama a kudancin kasar nan muga ya za’a yi a zauna lafiya wadanda aka zalunta muga ta yaya za’a kwato musu hakkinsu su kuma wadanda suka yi zuluncin muga ya za’ayi a hukunta su domin baiwa kowa Hakkinsu”
” Mun shiga gaba wajen ganin ya za’a warware bakin fentin da ake shafawa fulani wanda ake ganin kowanne Bafulatani dan ta’adda ne ko dan garkuwa da mutane ne saboda rashin adalci ne a yi wa al’umma guda daya jam’u wanda Bai kamata ba”.
Kungiyar mu ta himmatu wajen tattaunawa da gwamnati muga yadda za’a warware matsalar da ke tsakanin fulani da kuma Gano shin ta Ina ne matsalar take da kuma sanin su wanene ke da alhakin matsalar da kuma sanin yadda za’a magance matsalolin kuma insha Allah tattaunawar mu tayi Nisa a kan hakan” inji shi.
Da yake bayani a kan samar da jami’an tsaro na ‘Yan Sa kai, shugaban ya ce akwai alfanu a cikin tsarin muddin za su bi dokokin da suka kamata wajen tallafawa harkar tsaron.
Ya kara da cewa idan har Askawaran tsaro irin na jihar Zamfara da Jihar Katsina za su bi hanyoyin da suka kamata, babu shakka za’a samu saukin matsalar rashin tsaro a Arewacin Nijeriya, yana Mai cewa wuce gona da irin daga wurin jami’an tsaron sa kai shi ne ke taimawa wajen Lalata lamuran tsaro.