Home / Big News / MAJALISAR ZARTARWAR JIHAR BAUCHI TA SAUYA SUNAN JAMI’AR JIHAR DA SUNAN MARIGAYI MALAM  SA’ADU ZUNGUR

MAJALISAR ZARTARWAR JIHAR BAUCHI TA SAUYA SUNAN JAMI’AR JIHAR DA SUNAN MARIGAYI MALAM  SA’ADU ZUNGUR

MAJALISAR ZARTARWAR JIHAR BAUCHI TA SAUYA SUNAN JAMI’AR JIHAR DA SUNAN MARIGAYI MALAM  SA’ADU ZUNGUR
Majalisar zartarwa ta Jihar Bauchi a ranar Laraba ta amince da sauya sunan jami’a Mallakar jihar da sunan Marigayi Sa’adu Zungur.
Kwamishinan ilimi, Dr. Aliyu Tilde ya bayyana haka wa manema labarai Bayan kammala zamanta wadda Maigirma Gwamna Bala Muhammad Abdulkadir ya jagoranta a dakin taro na Gidan Gwamnati.
Dr. Aliyu Tilde ya ce sauya sunan nan ba da jimawa ba za’a Sanar da dukkan hukumomin da abin ya shafa da Kuma sanar da hukumar dake kula da jami’oi Kan cigaba da aka samu.
Wannan ranace mai cike da tarihi Kan ilimi a jihar Bauchi, Marigayi Malam Sa’adu Zungur mutum Ne Mai nagarta, Kuma Dan siyasa ne masanin tarihi wadda yabada gudumawa na tallafi kan karatu a jamhoriyar Arewa wadda a lokacin kafin karban yan’ci da gwagwarmaya da akayi Nigeria .
Munyi hakane don musauya sunan da Malam Sa’adu Zungur, wadda aihin dan’ jihar Bauchi ne Kuma na daya daga cikin Shuwagabannin da sukayi gwagwar mayan karba Mana yan’ci.
Kwamishinan yace wannan cigaba yaxo ne biyo bayan Tattaunawa da Ma’aikatan ilimi da Yan’uwa da iyalan Marigayi Malam Sa’adu Zungur wadda suka roki da aduba tayadda za’a girmama shehun Malamin.
Dr. Tilde wadda ya bayanna cewa Marigayi Malam Sa’adu Zungur wadda shine Maigidan Malam Aminu Kano a siyasa, Kuma shine sakataren NCNC , Kuma cikakken dan’siyasa ne wadda yasahara wajen chanxa da tsari yanayi yadda muke ake gudanar da Siyasa a yankin Arewa wadda har yanzu ana anfana dashi, sauya sunan Jami’an da sunansa anyi hakane don Kara Masa mutunci dayake dashi.
Kwamishinan Ayyuka da Sufuri, Honourable Abdulkadir Ibrahim (Cika Soron Bauchi) yayi magana Kan takarda da yagabatar wa Majalisar zartarwa na bada dama don cigaba da ayyukan hanyoyi da aka sa cikin kasafin dakayi na zangon karshe daya gabata na Shekarar 2020 Kuma anbada damar a cigaba.
Anata bangaren, Kwamishinan Kasuwanci , Honourable Maryam Garba Bagel tace dalilin kawo sabon Hukuma Mai suna Bauchi State Bureau for public
Privatization saboda shigo da yan’ kasuwa da masu saka hannun jari cikin Gwamnati don asamu cigaban tattalin arxiki.
Ta bukaci al’ummah dasu fahimci Wannan kokari na Maigirma Gwamna sannan su yabamasa na kokari dayakeyi don sauya jihar Bauchi da Samar da aikin yi wa dumbin al’ummah da muke dashi.
Anasa jawabin, Shugaban Hukumar Bauchi State Bureau of Public privatization & Economic Reform, Ibrahim Mohammad Kashin yace an Kirkiro Hukumar ne don ta taimaka wajen dawo da tattalin arxiki da bunkasa jihar.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.