Home / Labarai / Allah Ya Yi Wa Sale Bayari Shugaban Gan Allah Rasuwa

Allah Ya Yi Wa Sale Bayari Shugaban Gan Allah Rasuwa

Allah Ya Yi Wa Sale Bayari Shugaban Gan Allah Rasuwa

 

Mustapha Imrana Abdullahi

Bayanan da muke samu na cewa Allah ya yi wa shugaban kungiyar Fulani ta Kasa Gan Allah Fulani Development Association Of Nigeria, ( GAFDAN) Alhaji Sale Bayari  Bauran Wase rasuwa.
Bayanin hakan na cikin wata sanarwar da babban sakatare Janar na kasa Ibrahim Abdullahi ya fitar a cikin daren nan.
Inda ya bayyana sanarwar cewa marigayin ya rasu ne a yau da Yamma a garin Jos.
Sanarwar ta ci gaba da bayanin yi wa marigayin addu’ar samun rahamar ubangiji tare da samun Aljannah Firdaus.
Allah kuma ya ba iyalai,abokai,yan uwa da masu yin fatan alkairi hakurin jure wannan rashin na Alhaji Sale Bayari, Bauran Wase.

About andiya

Check Also

The Second Round Of Polio Commences On 20 to 23 APRIL 2024

  Parents and caregivers have been charged to ensure they make their children less than …

Leave a Reply

Your email address will not be published.