Home / Labarai / Majalisar  ZartaswarJihar Yobe Ta Amince Da Ware Naira  Biliyan 7.7 Don Gudanar Da Muhimman Ayyuka. 

Majalisar  ZartaswarJihar Yobe Ta Amince Da Ware Naira  Biliyan 7.7 Don Gudanar Da Muhimman Ayyuka. 

 

Daga Sani Gazas Chinade, Damaturu

 

 

Majalisar zartaswar jihar Yobe ta amince da ware kudi Naira biliyan 7, 771,564,656.32 domin gudanar da wasu manyan muhimmancin ayyuka a jihar.

Gwamnan jihar Mai Mala Buni ne ya jagoranci taron a fadar gwamnati dake Damaturu ranar Alhamis.

 

Da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala taron, kwamishinan ma’aikatar harkokin cikin gida yada labarai da al’adu na jihar Yobe, Alhaji  Mohammed Lamin, ya ce bayan tattaunawa kan batutuwa da dama da suka shafi jihar, sun amince da kafa asusun tallafawa ilimi na jihar Yobe (YETFUND)  hanyoyin gudanar da ayyukanta daban-daban don aiwatarwa don inganta rayuwar jama’a da inganta yanayin lafiya da ilimi na ‘yan Jihar.

 

Kwamishina Lamin ya kuma bayyana yadda Majalisar zartaswa ta amince da ware kudi N4,527,657,292.00, domin siyan magunguna da kayan aikin jinya, kayan Asibiti da samar da iskar oxygen/bututun magani a bangaren Lafiyar Mata da Yara, a asibitin Koyarwa na Jami’ar Jihar Yobe da dai sauransu

About andiya

Check Also

Group Decries Escalation Of  Insecurity In Birnin Gwari

      By; Our Reporter in Kaduna   The Birnin Gwari Progressive Union(BEPU) has …

Leave a Reply

Your email address will not be published.