Daga Imrana Abdullahi
A kokarin ganin an samar da al’umma sahihiya tagari da Mazon Allah Annabi Muhammadu (SAW) zai yi alfahari da ita a ranar gobe kiyama ya sa babban mai taimakawa Gwamnan Jihar Kaduna a kan harkokin addinai da samar da kyakkyawar dangantaka a tsakanin al’umma Shaikh Abdurrahaman Zakariyya Usman ya kafa katafariyar makarantar da ake koyawa kananan yara karatun haddar Kur’ani da suke samun nasarar haddacewa a cikin kasa da shekaru Goma sha biyar wato dai kafin su kammala karatun makarantar Sakandare ba
An dai gudanar da saukar mahaddatan ne a babban dakin taro na wurin yin musabakar Kur’ani da ke Unguwar Yan tukwane Kinkinau cikin garin Kaduna a arewacin tarayyar Najeriya.
Da yake bayar da tarihin makarantar Shaikh Abdurrahaman Zakariyya, ya ce makarantar dai sun fara yin ta ne suna yin karatu a cikin Falon gidansa da yara masu karatun yin haddar da ba su wuce biyar zuwa Bakwai ba kuma a tare da mai dakinsa suka fara, amma a yanzu makarantar HADDAR ta kai ga dalibai a kalla dari uku, wanda daga cikinsu a halin yanzu a wannan shekarar aka samu dalibai sama da Ashirin sun haddace Alkur’ani mai tsarki.
Shaikh Abdurrahaman ya kara da ankarar da jama’a cewa taimakawa maraya abu ne da ya zama wajibi, wanda sakamakon hakan muma muka Karrama wadansu iyaye musamman saboda abin da ya shafi marayu, muna da kimanin marayu Sittin da wani abu a wannan makaranta da muke daukar nauyinsu, muka bude sashi na musamman domin mu ba su haddar Kur’ani ba tare da an karbi ko kwandala a hannunsu ba. A yau dinan an samu kusan biyar daga cikinsu sun haddace Kur’ani kuma sun yi sauka kuma a wannan ne nake yin godiya ta musamman ga maigidana Gwamna Malam Uba Sani a lokacin da ya halarci wannan taron a shekara ta 2021 da ya ji labarin wannan abu tun da daman Uba ne ga marayu nan take ya dauki nauyin haddar karatun dalibai 20 wadanda suka kasance marayu kuma a cikin daliban da Gwamna Uba Sani ke daukar nauyinsu an samu guda biyar sun kammala haddarsu ta Kur’ani, saboda haka ina godiya ta musamman ga mai girma Gwamna Allah ya saka da alkairi”.
“Lallai kuwa Tallafawa maraya abu ne da ya zama wajibi a gare mu baki daya domin babu wanda ya san Gawar fari idan ka yi kamar yadda ka yi haka za a yi maka wato yadda ka shuka haka zaka girba don haka, ina yin kira azo a hada karfi da karfe a taimakawa marayu a kan abin da ya shafi ilimi da sauran abin ya shafi sauran al’amuran rayuwa
Ita dai wannan makaranta ta Koyar da hadda da kuma koyawa yara karatun Allo an kafa ta ne tun shekaru a kalla Bakwai, kuma akwai wadansu tsare tsare da aka fito da su a kalla guda biyar wanda a cikinsu aka kaddamar da yin karatun HADDAR Kur’ani ta hanyar yin karatu daga gida wato ta yanar Gizo.
A kokarin ganin yara sun haddace Kur’ani kafin su balaga makarantar ta fito da abubuwa biyar kamar haka;
Bangaren karatun Allo hade da kuma karatun boko
Sai kuma yin karatu sosai ba kama hannun yaro da za a haddace Kur’ani a cikin lokaci kadan.
Yin karatun haddar Kur’ani ta hanyar yin karatu ta yanar Gizo domin wasu daga cikin iyaye na son yin karatun don haka za su samu damar yin hakan.
Sai kuma bangaren karatun Islamiyya a Koyar da yara tsarki da sauran ayyukan Ibadar bautar Allah.
A wajen wannan gagarumin taron jama’a da dama da suka hada da shehunnan malaman addini da na Boko duk sun samu halarta kadan daga ciki sun hada da Shaikh Rabi’u Ganganba, Shaikh Asadussunah, Dokta Shehu Makarfi da dai sauran manyan malaman addini da dama.
Sai kuma daga cikin yan siyasa yan majalisar dokoki na Jihar Kaduna ba a barsu a baya ba domin kuwa sun samu halarta tare da shugaban majalisar dokokin Jihar Kaduna Yusuf Dahiru Liman, Malam Jamilu Abubakar Albani wakilin mazabar basawa sabon garin Zariya,Nasiru daga Tudun Wada Kaduna, sai kuma dan majalisar mazabar Kawo duk a cikin garin Kaduna dukkansu domin su kara girmama Kur’ani mai tsarki.
An kuma fadakar da jama’a cewa lallai babu shakka ko wani kokwanto babbar daraja itace yin riko da Alkur’ani mai tsarki.
Dubban jama’a ne Maza da Mata ne suka halarci gagarumin taron saukar karatun HADDAR kur’anin da yara Maza da Mata masu kananan shekaru suka sauke haddar a kasa ko a cikin shekaru sha biyar (15).
Abin da muka lura da shi dai shi ne duk wanda ya halarci wurin ya ta fi gida cike da farin ciki da annashuwa ganin irin yadda yaran suka yi karatunsu na hadda a bainar jama’a.
Kasancewar yadda jagoran makarantar ya ce hakika ba su ba duk wani Malami malanta sai ya kasance gangaran a haddar Kur’ani mai tsarki, domin ba yadda mutum zai bayar da abin da shi ba shi da shi kamar yadda yazo a cikin zantukan magabata