Related Articles
Masari Ya Sanya Wa Daura Dokar Hana Fita
Mustapha Imrana Abdullahi
Gwamnan Jihar Katsina Aminu Bello Masari ya Sanya wa garin Daura dokar hana fita dare da rana domin yin yaki da cutar Korona bairus da ke toshe Numfashi tare da haddasa matsaloli.
Kamar dai yadda Gwamnan ya bayyana cewa dokar za ta fara aiki ne da misalin karfe Bakwai na safiyar ranar Asabar mai zuwa.
Alhaji Aminu Bello Masari ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da manema labarai a game da batun lalubo mutanen da suka yi mu’amala da Likitan da cutar ta kashe a garin na Daura.
A cikin mutane 23 da aka dauki samfurin jininsu da aka aike wa cibiyar Gwajin jini ta NCDC ta kasa da ke Abuja, Gwamna Masari ya fayyace cewa an gano mutane 3 da suka kamu da alamar cutar Covid – 19 kuma sune ainihin matan Likitan da ya mutu da yayansa biyu.
Sakamakon faruwar wannan lamarin ya ci gaba da cewa tuni kwamitin aiki da cikawa karkashin mataimakin Gwamna da kuma sauran masu ruwa da tsaki suka yanke hukuncin cewa ga irin matakan da za su dauka domin hana yaduwar cutar Covid – 19 a tsakanin al’ummar Jihar.
Gwamnan ya kara da cewa za a bude shagunan nagano da kuma manyan shagunan magani guda uku, sai kuma wuraren sayar da hatsi da kayan abinci guda uku dunks su kasance a bude lokacin dokar hana fitar a Daura.
“Tuni aka bayar da izini ga jami’an tsaro domin su tabbatar da kiyayedokar da Gwamnati ta kafa, ya ce dukkan karamar hukumar da aka samu da cutar Covid – 19 za a kafa mata dokar hana fita dare da Rana kamar yadda aka yi wa Daura a halin yanzu.
Ya bukaci al’ummar Daura Daura su bayar da cikakken hadin kai da goyon baya ga wannan dokar ta zama a gida domin kiyaye lafiyarsu.