Home / Labarai / MATASA SU GUJEWA BANGAR SIYASA – ALIYU YA’U DOGARA GA ALLAH

MATASA SU GUJEWA BANGAR SIYASA – ALIYU YA’U DOGARA GA ALLAH

DAGA  IMRANA ABDULLAHI

Alhaji Aliyu Ya’u Dogara ga Allah fitaccen dan kasuwa ne da ke Kaduna ya yi kira ga daukacin matasa da su gujewa duk wani da zai Jefa su a cikin Bangar siyasa.

Aliyu Ya’u Dogara ga Allah ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a Kaduna, inda ya ce zaman lafiya fa ya fi zama dan Sarki kuma babu wani abin da za a hada shi da zaman lafiya domin sai da shi ne komai ke gudana a rayuwar duniya.

Alhaji Dogara ga Allah ya ci gaba da cewa duk wani dan siyasar da ke tunzura matasa yin Bangar siyasa ya na yi ne kawai domin samun biyan bukatar kansa kawai, don haka a hadu a zauna lafiya shi ne mafita.

“Muna fadakar da matasa cewa duk wanda ya yi zabe a ranar zabe ya koma gida kawai ya yi zamansa, don jada wani ya rude shi, saboda duk wanda zai ci Allah ya rigaya ya bashi zaben tuni”, inji Aliyu Ya’u.

Da yake tofa albarkacin bakinsa kuwa game da karramawa da kuma yadda wasu mutane suka rubuta tarihin Alkalin Mando kuwa, ya ce hakika ya Gamsu da wannan tsarin domin Alkalin ya cancanci ayi masa duk wata karramawa.

“Na san wannan Alkalin ne shekaru biyu da suka gabata don haka duk abin da mutum yake yi lallai adalcinsa ne kawai zai taimaka masa har al’umma su samu albarkacin kyawawan aikin da yake yi”, inji Aliyu Ya’u Dogara ga Allah.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.