Home / MUKALA / Matsalar Ruwan Fanfo A Sakkwato Da Kalubalen Rayuwa.

Matsalar Ruwan Fanfo A Sakkwato Da Kalubalen Rayuwa.

Yusuf Dingyadi, Sokoto
Kasancewar Ruwa da ake yi wa kirari da abokin aiki wanda babu wani mahaluki a dukkan fadin duniya da ke adawa ko baya so ko kin yin amfani da ruwan sha ko kuma duk wani ruwa mai tsafta da za a iya yin amfani da shi a tsaftace mutum dan Adam ko kuma ya tsafta ce Tufafi, wurin zama ko amfani ko dukkan abin da dan Adam zai yi amfani da shi a fadin duniya, a saboda haka ne al’ummar Jihar Sakkwato da ke zaune a arewacin tarayyar Najeriya suke koka wa a game da irin halin da ake ciki na karancin ruwan domin amfani da kuma gudanar da rayuwa.
Hakan ta sa wani marubuci kuma mai sharhi a kafafen yada labarai na rediyo, Talbijin da jaridu Malam Yusuf Dingyadi ya dan yi tsakure a game da irin halin da ake ciki da kuma kokarin fadakarwa domin Gwamnati ta rika yin amfani da shawarwarin kwararrun masana da suka fahimci matsalar ruwa da hanyoyin magance ta domin amfanin jama’ar birni da karkara.
Muddin aka ci gaba da rufa-rufa, ba a dauki shawara masana aikin sanin makama akan samar da ruwan sha b a Sakkwato, to tabbata, har yanzu akwai matsaloli tattare da samar da ruwan issasu ga al’umma.
Rashin daukar shawarwarin da tsoffafin kwamishinonin ruwa suka bayar, mussaman irin su Honarabul Umar Bature don sake fasalta aikin gidan samar da ruwa da farfado da tsarin gyara da inganta bututun ruwa na  gidan ruwan Sokoto da maido da daraja ma’aikatan gidan ruwa na Sokoto; tabbata duk wani gyara na yanzu tamkar wucin gadi ne.
Daga cikin tsarin sa har da neman gwamnati ta gina kananan tashoshin samar da ruwan sha a cikin manyan unguwani wadanda zasu samar da ruwa daga manyan rijiyoyin Burtsatse  da za a gina irin na zamani don aikawa ga unguwanin dake da nisa da gidan ruwa ko tashoshin su.
Haka ma akwai kara kudaden tallafi na mussaman kai tsaye daga ofishin gwamna zuwa hukumar samar da ruwan sha ta jiha da gina kananan rijiyoyin burtsatse ga al’umma.
Haka ma akwai matakin hukunci ga wadanda suka gina reservoir na tara ruwa a gidajensu, don tasu biyan bukata, inda suka hana talakawa samun issasun ruwan da ake turawa na Fanfo daga tashoshin samar da ruwan na tsohuwar kasuwa, Ali Akilu, Tasha Illela da Runjin Sambo.
Kwamishinonin ruwa Hon Bature da Honarabul Yabo, duk sun mayar da hankali kacokan ga bin tsarin hanyoyin bunkasa samar da ruwa da aiki kafada kafada da kwarrarun ma’aikatan gidan ruwa da suka yi wa Gidan Ruwa na Gwamnati aiki a baya, don samun shawara na bunkasa wannan aikin na samar da ruwan sha a Sokoto cikin dan lokaci.
Daga galan miliyan biyu zuwa hudu yanzu ana bukatar fiye da galan miliyan goma don amfanar da jama’a; sai kuma bukatar bunkasa aikin gidan ruwa na Asari wanda tun farko ake zargin gwamnatin Wamakko tayi coge garesa, da sake fadada gidan ruwa na Runjin Sambo, wadanan duk muhimman ayyuka ne dake da tasiri ga samar da ruwan sha ga al’ummarmu.
Ya dace Hukumar samar da ruwan sha ta dawo da karba kudaden ruwa ta amfani da hanyoyin zamani a maimakon dogara ga kudin shiga daga ma’aikatan gwamnati da kamfanoni kadai.
Yana da kyau kamin Gwamna ya nada Kwamishina da zai kula da ma’aikata ruwa yayi garambawul baki daya ga hukumar samar da ruwan sha ta jihar Sokoto, ya sake fasalta aikin ta, ya dauko masu ‘Contract ‘ tsoffafin ma’aikatan da suka yi hobbasa a baya don ganin sun maido da daraja hanyoyin inganta samar da ruwan sha a birni da kauyuka.
Haka ma a rushe gine gine da akayi akan manyan bututun dake kai ruwan sha a cikin gari da sake sabunta wasu daga ciki da tsufa ya hana su aiki.
Tsarin nan na Honarabul Umar Bature da Engr Shehu Mafara sune muhimman hanyoyin da za su ceto Jihar Sakkwato daga ci gaba da fuskantar barazana karancin ruwan sha. A yanzu da lamarin dimmamar yanayi ke kara ta’azzara ga duniya baki daya.
Lokaci yayi da zamu aje mummunan fahimta ta dora laifi ga gwamnati ita kadai, akan abin da ya shafi karancin ruwan sha, don kuwa yanzu ya zama darasi akan wadanda suke zargin gwamnatin Tambuwal da zama dalilin haka.
Zancen biyan kudaden bashi na hukumar samar da wutar lantarki, wannan duk buge ce, muhimmin abin da ya dace, Gwamnatin Jihar Sakkwato ta gaya ma al’umma gaskiya akan matsalolin da ke tattare da aikin samar da ruwan sha da rarraba shi.
Matsalar yanayi da rashin issasun ruwa daga ainihin gulaben dake kawo ruwan kamin tace su; tsadar kayan gyara da karancin kudaden tallafi na aiki ga hukumar samar da ingantacce kuma wadataccen tsaftataccen ruwan sha ta Jiha,da sauransu na daga cikin ababen da ya dace ayi ma jama’a bayani dalla dalla.
Su kansu al’umma suna da nasu laifi a kan batun rashin biyan kudaden ruwa da na tallafi da ake nema, wasa da ruwan sha da yin ko oho ga gyaran bututu a unguwaninsu da sauran matsalolin da ke barazana ga samun ruwan sha.
Allah Ya kawo MAFITA Game da wannan lamarin na karancin ruwa da ya haifar da wahala.
Yusuf Dingyadi, Sokoto

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.