Related Articles
Matsalarmu Ita Ce Rashin Alkali Tsakanin Kamfanonin Waya Da Masu Hulda Da Su – Fantami
Imrana Abdullahi
Ministan kula da harkokin Sadarwa da bunkasar tattalin arzikin kasa ta hanyar sadarwa Furofesa Isa Ali Fantami ya bayyana cewa babbar matsalar da suke fama da ita a halin yanzu itace ta rashin wata sahigiyar na’urar da za ta zama Alkaliya tsakanin kamfanonin wayoyin sadarwa da masu hulda da su.
Ya ce idan a misali “Idan wani mutum ya yi korafin an janye masa kudi a layin wayar da yake amfani da shi ko aka janye masa Data, to, babu wata hanyar da za a yi amfani da ita a gane sai dai kawai irin rahoton da za a samu daga wurin kamfanin wayar daga na’urorinsu kawai, shi mai huldar da su bashi da wata hanyar na’urar da za ta nuna yadda lamarin ya gudana, wanda hakan yana zamar mana wata matsala kwarai”.
Minista Fantami ya ci gaba da cewa suna nan suna kokarin ganin an samar da wata sahihiyar na’urar da za ta zama kamar Alkali a tsakanin kamfanin waya da masu hulda da shi domin a yi wa kowa adalci.
Ya dai bayyana hakan ne a lokacin da yake tattaunawa da kafar yada labarai ta Muryar Amurka sashen hausa inda ya ce an samu gagarumin ci gaba a harkar sadarwa da ma’aikatar da yake yi wa jagoranci, kuma a kullum suna kokarin kara inganta al’amura domin yan kasa su ci ribar lamarin.