Home / Labarai / Mun Kashe Batun Yarjejeniyar Samowa A Majalisa

Mun Kashe Batun Yarjejeniyar Samowa A Majalisa

Yan majalisa sun yabawa takwaransu Ali Madaki daga Kano

Daga Bashir Bello majalisar Abuja

Dan majalisa Inuwa Garba mai wakiltar mazabar Yamaltu Deba daga Jihar Gombe ya yabawa takwaransa Ali Madaki sakamakon kudirin da ya kawo game da batun yarjejeniyar Samowa, da ya bayyana da wata fitinar da ta tunkaro Najeriya.

Dan majalisa Inuwa Garba ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a Abuja.

Inuwa Garba ya ce hakika ya dace a yabawa dan majalisa Ali Madaki daga Jihar Kano da ya kawo wannan batu a gaban majalisar wakilai domin a hanzarta tattauna dukkan batutuwan da ke kunshe a cikin kudirin kamar yadda ya ce wata fitina ce da ta tinkaro kasa.

Inuwa Garba ya ci gaba da cewa ita dai wannan yarjejeniya ta Samowa na cike da abubuwan tsoro da suke a matsayin fitina a kasa baki daya, dole ne mu a matsayin mu na wakilan jama’a mu yi wa Ali Madaki godiya kasancewarsa mutumin da ya yi Zakara ya kawo batun gaban majalisa har ma aka tattauna sannan aka yi fatali da shi, kasancewar tsarin ya ci karo da irin yanayi da tsarin mutanen da muke wakilta a wannan majalisa ta wakilai

“Yankin mu da addinin musulunci da na Kirista duk ba su amince da wannan tsarin ba”.

Saboda haka ne muke yin kira da cewa lallai ya dace a bi yanayi da tsarin da dokar kasa ta tanada kafin a yi duk wata yarjejeniya kamar dai yadda tsarin ya ce sai an kawo wa majalisa idan za a yi wata yarjejeniya don haka majalisa fa ba ta Sani ba sa.

“Babu wani mahaluki mai hankali don ban ce kowa da kowa ba da zai amince da cewa wannan yarjejeniyar Samowa ba fitina ba ce, domin sharri aka kulla in ko ba haka ba ai da an bi yadda dokar kasa ta tanadar. Amma kawai sai muka ga an yi cushe kawai domin Namiji ya yi mu’amala da Namiji ko.Mace ta yi mi’amala da Mace in ma mutum ya ga dama ma zai iya yin mu’amala ko da Dabba ma don haka mu a ganin mu ko a tunanin mu bai yi dai dai da tsarin addinan Najeriya ba bai kuma yi dai dai da tsarin al’adu ko bukatun Najeriya ba. Kuma a Dimokuradiyya ko abu na da kyau idan har al’umma ta ce ba ta so hakika ya zama mummuna kawai”.

Inuwa ya fayyace cewa hakkin ta ne ta zamo wadanda za su wakilce ta ko Gwamnatin da za ta jagirance ta a koda yaushe, amma kuma ta na da damar ta ce ta na so ko ba ta so idan an kawo, amma kashi sama da Casa’in na al’ummar Najeriya sun ce basa so don haka annun da aka sa a cikin yarjejeniyar yau min yanke shi saboda haka muna yin kira a fito a soke wannan sa hannun da aka yi kuma idan ma akwai mai son a kawo shi gaban majalisa ko da an kawo sunansa Allah ya jikansa mun kashe shi an gama baki daya idan ma akwai wani abu da suke ganin yana da kyau a cikin wannan yarjejeniya to hakika kyaunsa ya lalace.

” Wani da da kudinsa zai je ya sayi Nama ya ci kuma wani da kudinsa zai je ya sayi gauta ya ce duk kuma sun ji dadi, mu a Najeriya halin da muke ciki rarrashin Ubangiji yakamata mu yi ba ba mu kara matsalar ba ta hanyar nuna wa Ubangiji cewa mun ginu a kan yin karan tsaye ba

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.