Home / Big News / Mun shirya Taron Ne Domin Fadakarwa Da Tallafawa Mata Masu Karamin Karfi – A’isha Yaba

Mun shirya Taron Ne Domin Fadakarwa Da Tallafawa Mata Masu Karamin Karfi – A’isha Yaba

 

Daga Imrana Abdullahi
An bayyana babban dalilin shirya taron mata da aka yi karkashin shirin HER 2026, da cewa an yi ne domin a taimakawa mata musamman masu karamin karfi da ke cikin al’umma.

A’isha Shehu da aka fi sani da Yaba ce ta bayyana hakan a lokacin da take tattaunawa da manema labarai jim kadan bayan kammala taron da aka yi a Kaduna.

Kadan daga cikin tarihi na shi ne Ni sunana A’isha amma an fi sani na da Yaba, kuma ina da aure da yaya Uku sannan ina kasuwanci, an haife Ni a garin Maiduguri na tashi a can amma a yanzu ina Kaduna don haka zan yi magana da ku yan jarida da Hausa da Turanci
“Mun shirya wannan taron ne domin mu tallafa wa mata masu karamin karfi, mun kuma fadakar da mata yanayin zamantakewa da yanayin Zaman Aure da yanayin zamantakewa tsakanin kawaye,yan uwa da kowa har ma da yadda za ayi magana duk a harkar rayuwa, an taimakawa mutane da yawa da akwai wadanda aka ba miliyan daya da akwai masu dubu dari biyar akwai masu dubu ɗari biyu ga sunana dai da yawa.
Ta kara da bayanin cewa a halin yanzu akwai tsarin yin rajistar da ake kai na mutane a ƙalla ɗari biyu da za a yi masu Tirenin wato horas wa a kan abin da za su koya kuma za a ba su kudin da za su yi sana’ar da shi.
” Muna fatan dukkan matan da aka ba wannan jarin ya amfane su ya yi albarka ya zama sanadiyyar arzikinsu  kuma duk fadakarwar da aka yi Allah ya sa ya yi mana amfani kuma duk wadanda suka taimake mu da yan Gwamnati, kawaye da abokanai har ma da yan uwa Allah ya ba su ladar, kuma wannan shi ne taron da na yi na farko a Kaduna.
A’isha Yaba ta kuma yi godiya ga daukacin al’ummar da suka halarci taron ciki har da Uwar gidan Gwamnan Jihar Kaduna da ya mikawa dukkan matan da suka amfana Cekin kudin da aka ba su.

About andiya

Check Also

SAKON ALHERI NA RAMADAN

  Daga Mai Girma, Jakada Dr. Malami Shehu Ma’aji (MFR) Shugaban, Kwamitin Shawara, Hukumar Kare …

Leave a Reply

Your email address will not be published.