Daga Imrana Abdullahi
GwamnanJihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya ce Gwamnatinsa, na yin iyakacin bakin kokarinta domin ganin sun tsare Amanar jama’a da aka Dora masu.
Gwamna Dokta Dikko Umar Radda ya ci gaba da bayanin cewa tun hawansu bisa karagar mulki, suke ta kokarin kawo tsarin toshe duk wasu kafofi da kudaden gwamnati ke zurarewa da gudanar da gwamnati ba tare da wata kumbiya-kumbiya ba.
Bayanin haka ya fito daga Isah Miqdad a ofishin Daraktan Yada Labarai a ranar 19 ga Yulin 2923.
Bayanin ya ceGwamna Radda ya sanar da hakan ne a gagarumin taron bita da Gidauniyar Jihar Katsina ta shirya na shekarar 2023 da ya gudana a gidan gwamnatin jihar Katsina a ranar Laraba, 19th Yuli, 2023.
Dokta Dikko Umaru Radda ya ce gwamnatinsa ta kuma bullo da tsare-tsare masu inganci da za ta tunkari matsaloli da kalubalen da jihar ke fuskanta, musamman a sha’anin tsaro, aikin gona, zaman kashe wando a tsakanin matasa da sauransu.
Ya bayyana Gidauniyar Jihar Katsina da cewa ta tallafa sosai wajen kawo ci gaba a jihar da kuma mara baya ga tsare-tsare da kudurorin gwamnati na saukakawa al’umma a harkokin yau da kullum.
Tsohon shugaban Nijeriya Muhammad Buhari, wanda shi ne shugaban Gidauniyar na farko, ya ce kwamitin amintattu hadin guiwa da majalisar mashawartan Gidauniyar ne suka shirya taron bitar domin zakulo sabbin fasahohin da za su kara habbaka ayyukan Gidauniyar.
Tsohon shugaban kasar ya ce amfanin wannan Gidauniya ba zai misaltu ba a Jihar Katsina, ganin yadda ta ba da gagarumar gudunmuwa wajen inganta tsaro da hadin kan al’umma.
Muhammad Buhari ya ce irin ci gaban da GidauniyarJihar Katsina ta kawo ga al’ummar jihar abin a yaba ne, kan haka ne ya yaba da irin hangen nesan kwamitin amintattu na Gidauniyar da ya shirya wannan taron bita.
Shugaban Gidauniyar Jihar Katsina, Dokta Umar Mutallab ya yi kira da a ba matasa dama domin su ba da tasu gudummuwa a cikin ayyukan Gidauniya domin ayyukanta su dore.
Ya yaba da yadda Gidauniyar Jihar Katsina ta farfado da kwamitin amintattu da take da shi da majalisar masu ba da shawara domin jihar Katsina ta ci gaba da amfana da ayyukan Gidauniya.