Mustapha Imrana Abdullahi
Gwamnan Jihar Salkwato Alhaji Aminu Waziri Tambuwal, ya bayyana cewa ya na goyon bayan irin Luguden Wutar da ake yi wa yan Ta’adda a halin yanzu.
Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana hakan ne a cikin wani faifan bidiyon da ya tattauna da kafar yada labarai ta Muryar Amurka sashen hausa, da Malam Yusuf Dingyadi ya aiko mana.
Sai dai ya ce tun da dadewa suka so a dauki irin matakin da ake dauka a halin yanzu amma abin bai samu ba sai yanzu.
“Mun so a dauki dukkan matakan da suka dace domin yin maganin yan Ta’adda da ayyukansu baki daya amma ba mu samu damar hakan ba sai yanzu , kuma mun so a dauki matakan ne a lokaci daya baki daya domin kada su samu damar kwarara su shiga wani wuri daga wurin da suke amma duk da haka a yanzu muna goyon baya kwarai”, inji Aminu Waziri Tambuwal.
Tambuwal ya ci gaba da cewa “ko wannan rufe layukan sadarwar da aka yi ai mu ne muka rubutawa Gwamnati wato ofishin ministan sadarwa Malam Isa Ali Fantami, domin a dauki matakin da aka dauka na rufe layukan sadarwar layukan wayoyin hannu a kananan hukumomi Goma sha Hudu (14).