Home / News / Muna Kira Ga Isa Ashiru Ya Ce A Ciyar Da Jihar Kaduna Gaba – Sardaunan Ikulu

Muna Kira Ga Isa Ashiru Ya Ce A Ciyar Da Jihar Kaduna Gaba – Sardaunan Ikulu

Daga Imrana Abdullahi

Malam Hassan Musa, malami ne a kwalejin ilimin Jihar Kaduna kuma Sakatare sannan  kuma shugaban babban kwamitin yada labarai na masoya Sardaunan Ikulu da ake kira (Sardaunan Ikulu Fans), ya ce sun halarci babban ofishin kungiyar APC Ciki da waje da ke tallata manufofi da irin tsare tsaren Gwamnatin APC karkashin jagoranci Gwamna Uba Sani.

Malam Hassan Musa ya ce Dokta Isma’ila Yusuf Ashafa, Sardaunan Ikulu, ya turo shi domin ya wakilce shi a game da wannan taron da aka shirya a babban ofishin APC Ciki da waje na Jihar kaduna domin taya Juna murnar nasarar da aka samu a kotun koli, inda ta tabbatar da nasarar zababben Gwamnan Jihar Kaduna Sanata Uba Sani.

A kan haka ne Sardaunan Ikulu, ya turo ni in wakilce shi ya kuma ce yana yin kira ga dan takarar Gwamna na PDP da ya zo a hada hannu domin yi wa Jihar Kaduna aiki a fannonin ciyar da rayuwa gaba.

“Nazo ne a matsayin wakilin Sardaunan Ikulu domin taya wannan babbar kungiya ta ciki da waje murnar nasarar da mai girma Gwaman Jihar Kaduna Uba Sani ya yi a kotun kolin tarayyar Najeriya, inda ta tabbatar da shi a matsayin zababben Gwamnan Jihar Kadun”.

” Shi Sardaunan Ikulu ya ce a gaya wa duniya cewa nasara ce da kusan kowa ya san da ita, saboda a watan Tara kotun sauraren kararrakin Zabe tirabunal ta yanke hukuncin cewa mai girma Uba Sani ne ya ci zabe, haka kuma a watan sha daya kotun daukaka kara a Abuja ta jaddada batun cewa Gwamna Uba Sani ne ya ci Zabe a lokacin da aka gudanar da zabe a shekarar 2023. Muna yi wa Allah godiya cewa a yau ma Juma’a lamarin ya sake tabbata kotun kolin Najeriya ta tabbatar da hakan a ranar sha tara ga watan daya, 2024, saboda haka halastaccen zabe ne don haka magana ce da kowa ya Sanya bayyananniya ba sai an yi Jeka la dawo ba”, inji Hassan wakilin Sardaunan Ikulu.

Hassan ya ci gaba da bayanin cewa sakon da mai girma Sardaunan Ikulu ya ce ya gaya wa abokan gamayyar siyasa shi ne “musamman babban dan takarar jam’iyyar Adawa na PDP honarabul Isa Ashiru Kudan shi ne yanzu kalubalen da ke a Jihar Kaduna ya wuce ace ana adawa daman duk lokacin da aka yi zabe wadansu abubuwan da zabe ke kawo wa nan da can don haka shi babban dan takarar PDP Isa Ashiru Kudan da sauran yan adawa da suyi hakuri a hada hannu domin a ciyar da Jihar da al’ummarta Kaduna gaba tun da an kai kotun koli kuma kotun ta yanke hukuncin ta don haka muna fatan shi Ashiru Kudan zai saurari wannan kiran kasancewar wannan kiran ba shi ne na farko ba ta yadda za a ciyar da Jihar kaduna gaba”, inji Sardaunan Ikulu.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.