Muna Kokarin Kafa Hukumar Da Za Ta Hada Hukumomi Wuri Daya Ne – Honarabul Gumi
andiya
July 24, 2024
Labarai, News
34 Views
Bashir Bello majalisa Abuja
Honarabul Suleiman Abubakar Gumi wakilin kananan hukumomin Gumi da Bukkum a majalisar wakilai ta kasa a karkashin jam’iyyar PDP ya bayyana kudirin da suka tattauna a gaban majalisa da cewa suna so ne dukkan hukumomin Gwamnati da ke kula da batun lafiyar jama’a a samar masu da wata sabuwar hukuma.
Suleiman Abubakar Gumi ya ci gaba da cewa wannan yunkurin da suke yi zai ba dukkan wuraren kula da lafiyar jama’a damar su rika tattaunawa a tsakaninsu ta fuskar kiwon lafiya da tsaron al’umma.
“Amma su wadannan hukumomin lafiya kowane ya na aiwatar da aikin sa ne kawai duk da cewa aikin daya na shafar aikin dan uwansa don haka ne muke kokarin lallai sai an hada kai domin a san abin da ya dace a kowa yaushe, misali a nan shi ne matsalar Gobara idan mutum zai gina kasuwa zai ta fi ya sayo kebil a Sanya tun da ba ka da wata masaniya a kan lamarin da zarar an samu wata matsala kawai sai dai mutum ya dauki asara. Kaga sai su masu aikin kwana kwana za su iya ganewa wane irin kaya ne aka yi aikin da shi akwai inda za su kai rahoto har a tambayi hukumar kula da inganci kayayyaki ta kasa ayi masu tambaya ta yaya suka bari kayan ya shigo Najeriya, kuma jami’an kwastan ya kuka bari har aka shigo da wannan kayan mara inganci cikin kasa dadai sauran wadansu hukumomi na Gwamnati duk irin wadannan tambayoyi ba wanda zai tambaye su domin kowanen su na yin aiki ne daban daban ba tare da yin aikin hada ka ba.
Don haka ne muka ga cewa idan akwai wata matattarar da za ta hada su kuma suna yin magana da junansu kaga hukumar kwana kwana masu aikin kashe Gobara idan sun ce akwai matsalar kebil da ke kawo gidaje na konewa kun ga za a kira masu hannu wajen kawo kebil din daga waje har zuwa masu amfani da shi a gidaje a tara su a kuma gaya wa kowa cewa lallai wannan ke kawo Gobara don haka a cire shi daga cikin kasuwa kun ga idan an samu yin wannan aikin za a kawo tsarin lafiya da kiwon lafiyar jama’a.
“Wannan hukumar da ake kokarin yi za ta tabbatar ne da cewa aikin ka fa zai iya shafar aikin wani misali idan jami’an kwastan ba su yi aikinsu da kyau ba komai zai iya shigowa a cikin kasa kaga yan Sanda za su iya cewa makamai sun yi yawa a cikin kasa kaga kwastan ne za a kira a tambaya. Kun ga idan wannan ya kaiwa shugaban kasa rahoton matsalar sa amma kuma ba yadda za a samu tattaunawa da wata hukumar da aikin ta ke shafar aikin wannan ta yaya za a warware matsalar
Kun ga a can baya ba wanda ke yin bayanin cewa idan an yi kaza da kaza lallai hakika kaza ne zai faru sai wannan hukumar da idan ana yi ko za a yi gini misali ka yadda kaurin gini da Kankare ya dace ayi ko kuma a batun idan an yi hadarin mota wani zai ce ga yawan hadarin da aka samu to wa zai tambaye su me yasa aka samu ragowa ko karin yawan hadarin idan an gano matsalar misali wata kwana ce keda matsalar sai su gaya wa ma’aikatar ayyuka domin a gyara matsalar ko kuma batun aikin soja musamman a wajen bangaren sakin Bam a wani wuri dole sai an tuntubi hukumar tukunna kafin ayi amfani da shi duk wannan haka muke kokarin yi