Home / Labarai / Muna Neman Taimakon Kungiyoyi, Masu Hannu Da Shuni – Iyayen Yara

Muna Neman Taimakon Kungiyoyi, Masu Hannu Da Shuni – Iyayen Yara

Muna Neman Taimakon Kungiyoyi, Masu Hannu Da Shuni – Iyayen Yara
Mustapha Imrana Abdullahi
Iyayen Yara dalibai da yan bindiga suka sace a babbar makarantar koyon aikin Gona da sanin ilimin Gandun daji ta Gwamnatin tarayya da ke Afaka karamar hukumar Igabi cikin Jihar Kaduna sun koka game da halin tsanani da ya haifar masu shiga tsaka mai wuya a cikin rayuwarsu.
Iyayen yaran sun bayyana halin da suke ciki ne ga manema labarai a wani taron da suka kira domin fayyacewa duniya halin da suke ciki sakamakon Sace yayansu da wasu yan bindiga suka yi lokacin da suke kusa da fara jarabawa a makarantar da ke karkashin ma’aikatar Muhalli ta tarayyar Nijeriya.
“Akwai lokacin da ministan muhalli ya zo Kaduna muka yi kokarin mu ganshi domin mu sanar masa halin da ake ciki game da Sace mana yaya amma ya ce shi ba zai yi magana da mu ba”.
“Wannan makaranta a karkashinsa take domin shi ne shugaban ma’aikatar Muhalli a Nijeriya kuma mun kawo yayan mu ne a makarantar Gwamnati ayi masu tarbiyya su samu ilimi domin su zama manyan gobe ta yaya wani zai zo ya kwashe mana yaya a hannun Gwamnati, amma its Gwamnatin har yanzu ta kasa yin komai duk an bar mu da wahala kawai”.
Sun shaidawa manema labarai cewa a halin yanzu yan bindigar da suka kwashe wadannan yaran su na kiran iyayen yara ne daya bayan daya domin sun ce su ba ruwansu da magana da Gwamnati su na kuma yi wa iyayen barazanar cewa za su kashe yaran nan kowa ya huta, wani lokacin kuma su na gaya wa iyayen yaran cewa za su aurar da matan kamar yadda aka aurar da na yan matan Chibok,
“Iyayen yaran nan ba su ma ko iya cin abinci wasu ma a halin yanzu su na fama da rashin lafiya, kuma su yan bindigar idan sun kira iyayen yara sai su rika kiran a kawo naira miliyan dari biyar ina iyayen yaran nan za su iya nemo naira miliyan dari biyar, wasu ma sana’ar Achaba suke yi fa saboda Allah fa, shi yasa muke rokon kungiyoyin kasa da kasa masu zaman kansu da dukkan wani ko wasu masu hannu da shuni su taimake mu yayan mu su fita daga cikin halin da suke ciki, don Allah muna rokon ku jama’a”.
Shugaban kungiyar iyayen yaran Mista Kambai da sakataren kungiyar Friday Sanni duk Sun kuma shaidawa manema labarai cewa a shirye suke a kai su kotu kamar yadda suka yi zargin Gwamnan Kaduna na cewa wai domin sun yi magana da yan bindigar da suka sace masu yaya.
“To ai gara a Jefa ni a cikin gidan Yari in dai yaya na za su fito ni ma wata rana zan fita daga gidan Yarin domin na san ba za a kashe ni ba,amma yanzu ina cikin wani mawuyacin hali na rashin kwanciyar hankali sakamakon sace mana yaya da yan bindiga suka yi”.
Wadansu iyayen dai musamman mata su na magana da manema labarai su na kuka sun ce ba abin da suke bukata sai a fitar masu da yayansu da suka kawo wa Gwamnati domin ayi masu tarbiyya a ba su ilimi amma suka kasance a halin yanzu a hannun yan banga.
Wata Uwa ta shaidawa yan jarida cewa yarta na cikin yara dalibai da aka saki amma tun a lokacin su na ta wahalar zuwa asibiti ne domin neman lafiyarta saboda tun lokacin ko abinci ba ta iya ci sai jigilar zuwa asibiti nan da can kawai.
Mista Friday Sanni, ya ce akwai lokacin da yan bindigar suka kira shi ya yi magana da yayansa biyu mata da aka sace aji yayan su na ta kuka, su na cewa a ba yan bindigar kudi na yi masu tambaya amma ban samu amsar komai ba, to ta yaya zan san halin da suke ciki kuma ni ina gida ta yaya zan iya cin abinci su su na can daji ana nuna su da bakin bindiga ana cewa za a harbesu Barbara da sun yi wani laifi ba haka kawai, jama’a ku taimaka mana don Allah, ba mu son a maimaita abin da ya faru da daliban makarantar Chibok a nan Kaduna.
“Shi yasa muke yin kira ga masu hannu da shuni, kungiyoyin kasa da kasa masu zaman kansu da su taimaka mana yayan mu su fita daga cikin halin da suke ciki a yanzu don Allah, saboda wasu iyayen ma da sun Sanya abinci ya shiga cikin cikinsu sai cikin ya harkace kawai saboda ba kwanciyar hankali.

About andiya

Check Also

Shekara Ɗaya A Ofis: Gwamna Lawal Ya Ƙaddamar Da Muhimman Ayyuka A Wasu Ƙananan Hukumomin Zamfara

  Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ƙaddamar da wasu muhimman ayyuka a Ƙananan Hukumomin …

Leave a Reply

Your email address will not be published.