By; Imrana Abdullahi
Kungiyar al’ummar Kudancin Kaduna (SOKAPU) ta bayyana bukatar da ke akwai na shugaba Bola Ahmad Tinubu ya dauki ministan tsaro ritaya Janar Christopher Musa a matsayin mataimakin sa a zabe mai zuwa.
Kungiyar ta bayyana hakan ne a wajen wani taron manema labarai da ya kira a Kaduna.

Kungiyar ta bakin shugabanta na kasa Injiniya Tabara Samuel Kato, sun yi kira ga shugaban kasa da ya duba wannan kiraye kirayen na su a zaɓen da ke ta fe ya dauki ministan tsaro Kiristopher Musa a matsayin mataimakin sa a zaɓen mai zuwa na shekarar 2027.
Tabara Samuel ya ci gaba da cewa ko a lokacin fa da aka naɗa ministan tsaro shugaban Sojoji duk al’umma sun yi ta murna da nuna farin cikin nadin, haka kuma a lokacin da shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya naɗa janar mai ritaya Christopher Musa a matsayin ministan tsaro duk jama’a ba tare da nuna wani bambanci ba suna ta murna da farin ciki.

Sai kuma Injiniya shugaban kungiyar SOKAPU na kasa ya bayyana murnar sa da irin goyon bayansu ga shugaban kasa da kuma Gwamnan Jihar Kaduna Kwamared Uba Sani a kan irin yadda suke kokarin tabbatar da tsaro da kuma jin dadi da walwalar jama’a
THESHIELD Garkuwa