Related Articles
Mustapha Imrana Abdullahi
Shugaban Kungiyar Masu Noman Zamani Ta Kasa NAMS honarabul Dokta Aliyu Muhammad Waziri San turakun Tudun Wada Kaduna na ta ya daukacin al’ummar musulmi baki daya murnar zagayowar ranar haihuwar
fiyayyen halitta Annabi Muhammadu (S.A.W).
Bayanin hakan ya fito ne daga bakin shugaban kungiyar masu Noman zamani ta kasa wato NAMS honarabul Dokta Aliyu Muhammad Waziri dan marayan zaki, Santurakin Tudun Wada Kaduna a cikin wani sakon murya da ya fitar domin ta ya al’ummar murna.
Alhaji Aliyu Muhammad Waziri ya ci gaba da bayanin cewa bikin Maulidi lokaci ne na Yabo,addu’o’i da salafi ga Manzon tsira don haka sai mu yi amfani da lokacin wajen yin addu’o’in neman zaman lafiya, karuwar arziki da ci gaba da fatan Allah ya maimaita mana