Home / Ilimi / MUNA YIN DIGIRI 17 A TSANGAYAR ILIMIN KARATU DAGA GIDA TA JAMI’AR AHMADU BELLO – FARFESA IBRAHIM SULE

MUNA YIN DIGIRI 17 A TSANGAYAR ILIMIN KARATU DAGA GIDA TA JAMI’AR AHMADU BELLO – FARFESA IBRAHIM SULE

Daga Imrana Abdullahi, Kaduna

Farfesa Ibrahim Muhammad Sule Darakta ne na tsangayar yin karatun digiri daga gida (Distance learning centre) da ke karkashin jami’ar Ahmadu Bello Zariya, ya bayyana cewa suna yin digiri guda Goma sha Bakwai 17 da suke yi a wannan cibiyar ilimi da yake yi wa shugabanci.

Shi wannan tsarin yin karatu daga gida ta yanar Gizo ba wani sabon abu ba ne idan an duba tarihin ilimi a Najeriya kuma  ga masu shekaru 50 zuwa 60 da ake yin wani tsari daga Landan ake kawo wa dalibai a nan suna rubuta jarabawa.

Kuma idan an duba a can baya kafin a fara jami’a ta farko da ke Ibadan domin ita ce jami’a ta farko a Najeriya, lallai idan za a iya tunawa akwai wasu mutane da suka karanta fannin Lauya kamar irin su Afe Babalola suk in ba a manta ba sun yi karatun lauyanci ne ta fanni irin wannan saboda haka a tarihin ilimi karatu daga gida ko karatu ta yanar Gizo ba wani abu ba ne sabo.

” An fara tsara shi daga gida sai kuma daga baya aka zo aka samu gidan rediyo suna karantar da dalibansu ta gidan rediyo har aka zo aka samu e-mail a yanar Gizo don haka wannan tsarin abu ne da aka fara shi tun da dadewa sai dai kawai ilimin kimiyya na ta canccan ca mashi tsari kawai tun daga lokacin da ake buga litattafai ana turawa ta gidan waya, rediyo da talfon har ga shi yau ana yi ta yanar Gizo don haka ba wani sabon abu ba ne ya na nan dindindin sai dai dan canjin da ake samu kawai.

Farfesa ya kuma ce hukumar da ke kula da jami’o’in Najeriya ta bayar da dama ga wannan cibiya da ke jami’ar Ahmadu Bello damar su yi digiri guda Goma sha Bakwai

Kuma a cikin wannan alkalumman akwai guda Tara da ake cewa digiri na farko sai Takwas kuma da suka kasance digiri na biyu kamar Masta digiri kamar kuma guda biyu ko uku kuma duk manyan digirori ne .

Da suka hada da digiri a fannin karatun kasuwanci, digiri a fannin mulki, sai karatun unguwar Zoma sai dai shi ba mu daukar daliban da suke da karatun sakandare sai wadanda suka kammala Difiloma, digiri a kan fannin kimiyyar siyasa, digiri a kan aikin akanta da digiri a kan karatun sanin halayyar dan Adam, digiri kan harkar tattalin arziki, digiri a kan karatun harkokin kasa da kasa ko kasashen waje da digiri a kan ilimin Kwamfuta.

A tsarin sai masta a kan ilimin kasuwanci, Alan karatun difilomasiyya Sato dangantakar kasa da kasa da kuma Masta a kan harkar kiwon lafiyar jama’a da kuma harkar ilimin doka da batun aikata laifuka kuma muna saran kafin jarshen shekarar nan za mu kara cikin yardar Allah.

” Tun lokacin da Obasanjo ya ba jami’ar yin karatu daga gida damar ta fara aiki tun a lokacin an yi doka a kasa da wanda ya yi digiri a jami’ar karatu daga gida da wanda ya yi digiri a cibiya ko Tsangaya irin wannan da kuma wanda yaje makaranta ya zauna ya yi digiri duk matsayi daya suke wato darajarsu daya ba wani bambanci ko an je  wajen daukar aiki duk darajarsu daya ne.

Kuma abin da mutum ke bukata idan ya na son a dauke shi a makarantar da kuma zuwa kundin koyarwar har lokacin da mutum zai kammala a bashi satifiket, ai kamar yadda na gaya maku duk abu daya ne duk wanda ya je makaranta ya zauna ya na yin gaba da gaba ne da Malami shi kuma wanda yake yin karatu daga gida baka yin fuska da fuska da malami kai tsaye kuan yi ne ta yanar Gizo amma akwai wurare biyu da dole sai an yi fuska da fuska a wuri biyu kamar yadda hukumar kula da jami’o’in ta bayyana domin ta karfafa cewa za a koyarwa yaro ta yanar Gizo amma a wuri biyu sai mutum ya zo an yi fuska da fuska da shi na farko shi ne a dan zauna a yi bitar abin da aka Koyar ta yanar Gizon sannan kuma na biyu akwai jarabawa hukumar ta jaddada lallai wadannan abubuwan biyu sai an yi su fuska da fuska wato gaba da gaba.

Farfesa ya tabbatarwa manema labarai cewa wannan tsarin ya taimaka wajen rage cinkoson jama’a a cikin jami’o’I saboda akwai wadansu kwasa kwasan da a can baya jami’a ba ta iya daukarsu amma a yanzu duk lamarin ya zama sai tarihi kawai domin suna ta daukar dalibai masu son yin karatun saboda saukin da aka samu.

About andiya

Check Also

Return Our Property, Documents In Your Possession, SWAN Tells Ex-President Sirawo

    The Sports Writers Association of Nigeria (SWAN) has warned its erstwhile National President, …

Leave a Reply

Your email address will not be published.