Related Articles
Daga Imrana Abdullahi
Kungiyar yan Arewa masu fafutukar samun ingantaccen shugabanci mai suna “Arewa Advocate For Good Governance”, sun jinjinawa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu bisa Namijin kokarin ganin Najeriya ta samu ci gaba a kowa ne fanni.
Shugaban kungiyar tare da wadansu mambobin kungiyar suka shaidawa manema labarai hakan a wajen wani taron manema labarai da aka yi cibiyar yan jarida da ke Kaduna.
Alhaji Jamilu Mato, a matsayin shugaban tafiyar ya ce sun zo cibiyar yan jarida ne domin yabawa tare da yin jinjina ga shugaban kasa bisa irin kokarin da yake yi na ciyar da kasar gaba.
Mato, ya kara da cewa irin kokarin da ministan ayyuka Sanata David Omahi a bisa aikin hanya da ake yi a Najeriya wanda ake yin hanyar ta hanyar amfani da kankare mai karfi da zai dade sosai ana yin amfani da shi kamar yadda dimbin masana suke yin bayani domin a fahimta”.
” duba da irin yadda shugaban ya bayar da aikin hanya daga Sakkwato zuwa Nadagry, wanda aikin babbar hanya ne da zai dade ana yinsa, wannan aikin zai hada dukkan bangarorin Najeriya baki daya daga nan Arewa zuwa Kudu Maso Yamma zuwa Kudu maso Gabas don haka muna yin jinjina kwarai ga ministan ayyuka Sanata, injiniya David Nweze Umahi da ya jajirce wajen ganin an samu nasarar da ta dace wajen gudanar da aikin.
Sai dai yayan kungiyar kamar yadda Alhaji Jamilu Mato ya shaidawa manema labarai cewa suna yin kira ga tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da ya ci gaba da bayar da cikakken hadin kai da dukkan goyon bayan da ya dace ga shugaba Bola Ahmed Tinubu somin samun nasarar da kowa ke bukatar samu, wanda muna ganin a matsayin Atiku na jigo a Najeriya hakan zai taimaka kwarai matuka idan ya bayar da goyon baya ga shugaban kasa.
Jamilu Mato ya kuma yi kira ga yan Najeriya ciki har da Atiku Abubakar da a rika rungumar Kaddara a koda yaushe.