Home / Lafiya / Mutane dubu dari biyu suka kamu da cutar Korona, Dubu 8 Sun Mutu A Duniya – WHO

Mutane dubu dari biyu suka kamu da cutar Korona, Dubu 8 Sun Mutu A Duniya – WHO

Hukumar kula da lafiya ta majalisar dinkin duniya (WHO) ta bayyana cewa a kalla mutane dubu 200,000 aka kawo rahoto a hukumar sun kamu da cutar Coronavirus (covid- 19)  sun kuma tabbatar da mutane dubu Takwas ne suka rasa rayukan sanadiyyar cutar .
Dakta Tedros Adhanom Ghebreyesus, Darakta Janar na WHO bayar da wadannan alkalumma a shafin hukumar na yanar Gizo.
Kamar yadda ya bayyana cewa sama da kashi 80 na rahotannin kamuwa da cutar daga yankuna biyu ne wato na tarayyar Turai da yankin Fasifik na Yamma.
“Muna sane cewa a yanzu kasashe da yawa na fuskantar matsalar raduwar cutar kuma suna cikin matsala a halin yanzu”.
“Muna jin ku. Kuma muna sane da irin mawuyacin halin da kuke ciki sakamakon wannan matsalar”.
Mun fahimci irin halin da zukatanku Duke ciki musamman dangane da zabin da zaku yi. “Mun fahimci cewa kasashe daban daban da suke da al’umma daban daban suna cikin yanayi mabambanta, a matakai daban daban na kamuwa da wannan cutar”.
Darakta Janar din ya ce hukumar lafiya ta majalisar dinkin duniya a halin yanzu tana magana da ministocin lafiya da kuma shugabannin kasashe da ma aikatan kula da harkokin lafiya da masu asibitoci da kuma masu masana’antu, shugabannin kamfanoni da cibiyoyi daban daban da dai sauransu duk ana magana da su a kowace rana.
“Hukumar lafiya ta WHO na magana da masu ruwa da tsaki domin taimaka masu su shirya don su bayar da muhimmanci, dangane da irin matakin da yanayin da suke ciki yake game da cutar coronavirus.
“Kada la yi tunanin cewa kai al’ummar da kake ciki ba za ta kamu da cutar ba. Don haka ka shirya kawai kamar akwai ta din kawai,la to shirin ko ta kwana kawai.
“Amma dai akwai kwarin Gwiwar cewa akwai abubuwa da dama da kasashe za su iya yi. Shi ne nisantar haduwa wuri daya sai kuma bayar da shawarwari a wuraren tarurruka da sula hada da manya manyan tarurruka zai taimaka wajen rage raduwar kwayar cutar.
” Kuma za a rage matsalar da ke kan tsarin kula da lafiya, domin za a iya shawo kan matsalar domin an dauki matakan da ya dace na hana yaduwarta, inji shi.
Bugu da kari, kamar yadda Darakta Janar din ya bayyana cewa dole ne kasashe su samu wani kebantaccen wuri da za a rika yin Gwaji da kuma duba marasa lafiyar da suka kamu da cutar kuma hakan zai bayar da damar a samu bibiyar saga inda wanda ya kamu da cutar ya fito ko wadanda ya yi hulda
“Hukumar lafiya ta WHO ta ci gaba da cewa yana da kyau cibiyoyin da aka ware domin kai marasa lafiyar da ake zargin sun kamu da za a bi sawun duk mutanen da wanda ya kamu ya yi hulda da su a kowace kasa ya dace suyi hakan.
“Wannan shi ne aka saran ya fi komai domin kare kamuwa da cutar domin kada a ci gaba da yada ta a cikin al’umma.
“Mafi yawan kasashen da suke da matsalar raduwar cutar hakika suna cikin matsayin da ya dace su dauki matakin yin hakan.
“Kasashe da yawa suna sauraren shawarwarin mu da kiraye Kirsten da muke yi masu domin samo lafiya hakan zai kara taimaka masu wajen kara himma su aiwatar da dukkan matakan da ya dace wanda hakan ya faru a kasashe da yawa”.
Kuma, Ghebreyesus ya ce wasu kasashe suna fama da raduwar matsalar kwarai ta hanyar kasuwar mutanen sosai da wannan cutar, tana mai cewa “mun gane yadda ya dace ayi domin hana raduwar cutar a yanayin da ake ciki. Amma za a iya yi”.
Darakta Janar din ya kuma godewa wadansu kasashen da suka bayar da goyon baya wajen tausayawa wuararen da sula kamu lamarin ya taimaka kwarai domin abin ya samu zuwa da sauki inda batta asi bitcoin da suke da matsalar cikowa duk sun bayar da gudunmawarsu.
Ya ce kasashe da yawa sun tabbatar da cewa za su shiga wasu ma tuni sun shiga shirin nuna tausayawa ga wadanda suka kamu. Kasashe irinsu Argentina, Bhrain, Canada, Faransa, Iran,Norway,Afirka ta Kudu,Spain, Switzerland da Thailand duk sun shiga kuma ina tabbatar da cewa karin wadansu ma za su shiga suma.
“Hakika zan samu jindadi da farin cikin ganin irin yadda wadansu kasashe ke nuna samuwa da irin yadda wadansu kasashen suka shiga sakamakon wannan cuta a duk fadin duniya baki daya.
“Asusun tallafa wa na wannan cuta ta COVID-19 ya samu nasarar samun sama da dalar Amurka miliyan 43 saga kasashen duniya sama da dubu 173,00 da kuma kungiyoyin duniya da dama duk sun tallafa.
“Yan kwanaki kadan da muka kafa gidauniyar taimakon zai iya godewa hukumar wasan kwallon kafa ta duniya FIFA game da taimakon da ta bayar na dala miliyan 10
“ Wannan da kuma wadansu da dama hakika sun bani kwarin Gwiwa cewa idan muka hada kai zamu iya cimma nasara
“ Wannan kwayar cuta na yi mana barazana amma kuma muna da dama muma ta mu hadu wuri daya domin yaki da ita domin makiyiyar mu ce da ke cutar da bil’adama” inji Darakta Janar

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.