Home / Ilimi / Gwamna Tambuwal Ya Bayar Da Umarnin Rufe Makarantu Na Kwanaki 30

Gwamna Tambuwal Ya Bayar Da Umarnin Rufe Makarantu Na Kwanaki 30

Imrana Abdullahi
Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na Jihar Sakkwato ya bayar da umarnin rufe makarantu baki daya har na tsawon kwanaki Talatin
Batun rufe makarantun zai fara ne daga ranar Litinin mai zuwa 23 ha watan Maris, 2020.
Daukar wannan mataki dai ya samo asali ne daga irin taron da aka yi na Gwamnonin Arewa maso Yamma a Kaduna inda aka dauki wannan mataki.
 Hakan na kunshe ne a cikin wata takardar da jami’in hulda da jama’a na ma’aikatar ilimi Nura Bello Maikwanci ya sanyawa hannu.
Kwamishinan ilimin Jihar Dakta M B Abubakar Guiwa ne ya bayyana hakan a cikin sanarwar ya ce rufe makarantun wani kokari ne na dakile cutar corona virus da ke yi wa duniya barazana.

About andiya

Check Also

Sultan urges muslims, Nigerians to reconcile selves for peace, unity says ‘don’t allow politics  divide you’

By Suleiman Adamu, Sokoto Ahead of the Ramadan fast around the corner, the Sultan of …

Leave a Reply

Your email address will not be published.