Home / Labarai / Mutane Su Daina Dogaro Da Yan Siyasa – Aliyu Waziri dan marayan Zaki

Mutane Su Daina Dogaro Da Yan Siyasa – Aliyu Waziri dan marayan Zaki

Daga Imrana Abdullahi
Dan marayan Zaki, San turakin Tudun Wada Kaduna kuma Kadimul Islam na kasar Hausa Alhaji Dokta Aliyu Muhammad Waziri, ya yi fadakarwa tare da jan hankali a game da batun tallafin rage radadin cire tallafin mai da kuma irin jajircewar da Malam Nasiru Ahmad El – Rufa’I tsohon Gwamnan Kaduna ya yi lokacin zamaninsa duk a tattaunawarsu da kafar Talbijin ta DITV da ke garin Kaduna, inda bayan yin cikakkun bayanai a kan al’amuran da suka shafi kasa Aliyu Waziri dan marayan Zaki, ya kuma amsa tambayoyin wadanda suka rika bugo waya a cikin shirin.
Lallai da an tambaye mu yadda za a yi a kan batun kudin tallafin man fetur da aka ba Jihohin Najeriya ai da mun bayar da shawarar yadda za a yi amma sai kawai wasu Gwamnonin da suke ganin sun iya komai to ba komai, har sai mutum ya sauka kamar yadda sauran da suka wuce suka sauka.
Da an tambaye mu cewa me za a yi da wannan biliyan biyar ta batun rage radadin tattalin man fetur da min fadi abin da za a iya yi da ita, to amma a lokacin da wani ke ganin shi ya iya ai sai ka rabu da shi kawai ya aiwatar da iya ta sa fahimtar.
“Hakika ka san Malam Nasiru Gwamna ne duk wanda ya kasance dan Jihar Kaduna ya san hakan, tun ranar da ya hau zuwa ranar da ya sauka kowa ya san shi Gwamna ne ba wata tantama a kan hakan, saboda ko Gwamnan Mulkin soja bai yi abin da Malam Nasiru ya aiwatar ba”.
Kai ko Gwamnan Soja da aka  yi a Kaduna bai yi abin da Malam Nasiru ya yi a matsayin Gwamna.
“Na rantse da Allah ko Gwamnan mulkin soja da aka fara a Kaduna bai yi abin da Malam Nasiru ya yi ba”.
Kai hatta da sauran Gwamnonin da yan Kaduna kowa ya san Gwamna ne tun ranar da ya hau har ya sauka  an san Gwamna ne wallahi, ko baya nan ka san ya na cikin zuciyarka ba ko tantama
Da jama’a sun san meye kungiyar kwadago ta Lebo hakika da ba haka ba domin su yan kungiyar kwadago muradunsu suke karewa kuma su a cikin yawan mutanen Najeriya ba su wuce kashi daya ba. Saboda haka muke yin magana kan cewa ” mu kuma sauran al’umma da ba ma’aikatan Gwamnati ba meye na mu muradun ko su kadai ne kawai mutane?
Saboda haka “ni na san meye kungiyar kwadago domin Babana da na tashi a hannunsa ai ya ta ba yin ministan kwadago a Najeriya kuma ni ne mai taimaka masa wato PA don haka na san kungiyar kwadago kwarai, ko shi Oshiomhole tun ya na nan Kaduna a Dirkaniya ma ya na kungiyar kwadagon duk na san shi sarai kuma mun san meye kungiyar kwadago kuma a kan me aka yi ta”.
“Mu abin da muke bukata shi ne duk abin da za a yi a yi shi bisa kishin kasa da adalci kuma meye kasa za ta ci gaba meye yan kasa za su ci gaba ba wai kawai me mutum zai samu ba. Sabida haka ina gaya wa jama’a cewa siyasa ake yi amma mutane sun kasa fahimtar meye ma siyasar.
“Na farko dai ba unguwar da bata da kansila kuma ba karamar hukumar da ba ta da dan majalisa kuma ga Sanata a kowace Jiha akwai guda uku duk fa wakilan jama’a ne, to, duk wadannan ba su yi maka maganin wani abu ba sai kungiyar kwadago da ke kare muradun ma’aikatan da ba su wuce kashi daya cikin dari na yawan jama’a ba, kuma duk da kankantarsu idan sun kare muradunsu ba muke sun yi laifi ba
Hakika Gwamnati na iya yin duk abin da take bukatar ta yi, saboda ta na da karfi domin Allah ne ya saukar da ita daga Allah sai Gwamnati. Amma jama’a su Sani cewa akwai abin da ya dace su yi fa domin su ci gaba.
“Ku duba da a kan batun karin kudin wutar lantarkin da ake Sayarwa jama’a suk yunit sai da na ta fi kotun Gwamnatin tarayya a Legas kuma kotu ma ta ce ba ta yarda a kara kudin ba amma duk da hakan bai hana komai ba sai da aka kara abin da ya fi duk kudin da muke tsammani”.
Aliyu Muhammad Waziri San turakin Tudun Wada Kaduna ta kara jadda yin kira ga jama’a kan bukatar da ke akwai cewa ya dace kowa ya nemowa kansa abin dabzai ciyar da kansa da iyalansa kawai shi ne mafita domin ma’aikatan majalisu da yan siyasar da ake da su a da can ne mutane ba kamar na yanzu ba da kowa kansa kawai ya Sani don haka dogaro da Allah ne mafita kuma zai iya ba mutum abin da ya fi nawa sau dari don haka kowa ya fita nema sau dari amma a daina yin tunanin cewa wai mutum ya zauna sai Gwamnati ta yi masa kaza ko kaza domin zama a hana nan yaudarar kai ne kawai kowa ya fita nema kawa.
Ya ce kowa ya tarbiyantar da yayansa domin a cikinsu akwai shugaban karamar hukuma kuma akwai yan majalisu har da Sanatoci ma duk akwai Gwamna ma amma ka fita daga layin yaudarar kai. Kuma ni a yanzu ba ajin da ba ni da da tun daga karamar makarantar rainon yara, Firamare, Sakandare zuwa jami’a duk ina da dalibai ko’ina kuma kamar yadda na ce a can baya shi ne mu dage da yi wa kasar addu’ar samun zaman lafiya da ci gaban tattalin arzikin kowa shi ne babban lamari

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.