Home / Labarai / Mutane Su Rika Mika Korafi Ta Hanyar Da Ta Dace – Aliyu Waziri Dan marayan Zaki

Mutane Su Rika Mika Korafi Ta Hanyar Da Ta Dace – Aliyu Waziri Dan marayan Zaki

Daga Imrana Abdullahi
Alhaji Dokta Aliyu Muhammad Waziri dan marayan Zaki kuma Santurakin Tudun Wada Kaduna ya yi kira ga daukacin al’ummar Najeriya da su rika mika korafinsu ta inda ya dace domin samun warakar matsalolin da ake korafin a kansu.
Dokta Aliyu Muhammad Waziri ya yi wannan kiran ne a cikin wata tattaunawa da ya yi na tsawon awa biyu da kafar Talbijin ta DITV Kaduna.
Dokta Waziri ya ci gaba da bayanin cewa shi a koda yaushe ya na yin kira ne ga jama’a idan za su mika korafinsu lallai su tabbatar sun mika shi a inda ya dace ta hanyar rubuta korafin a rubuce su mikawa dan majalisar da ke wakiltar su a matakin Jiha ko na tarayya.
“Idan abin da ya shafi Jiha ne su rika mika korafin ga shugaban karamar hukuma da dan majalisar Jiha domin ya Gabatarwa Gwamnatin jihar da suke. Idan kuma a matakin tarayya ne jama’a su rika mika korafinsu a rubuce ga dan majalisar tarayya ko Sanata kuma su shaida masa cewa za su kalli Talbijin domin ganin yadda zai gabatar da korafin na su a gaban majalisar kasa da nufin ayi masu maganin abin da ke daminsu”.
” Hakika akwai wahalar talauci da matsalar hau awards farashin kayan abinci da na masarufi a cikin al’umma kuma ya na idanunsu kwarai
Dan marayan Zaki ya kuma ce ayi hakuri tukunna domin lokacin bude shafin halin da Gwamnati ke ciki bai yi ba, amma da zarar Gwamnati ta yi watanni shida zuwa shekara daya to lokaci ya yi kuma za a yi wa jama’a cikakken bayani domin su fahimci abin da ake ciki.
Sai dai Aliyu Waziri Santurakin Tudun Wada Kaduna ya ce suna yi wa Gwamnatin tarayyar Najeriya karkashin jagorancin Bola Ahmad Tinibu kyakkyawan zato don haka kowa ya jira ya gani nan gaba.
A ci gaba da yin addu’o’in neman taimakon Allah da dukkan samun daukin da sauki daga Allah madaukakin Sarki domin tabbas akwai matsalolin talauci, Yunwa, rashin ilimi, rashin asibiti da matsalar tsaro don haka a dage da addu’a
A game da batun kudin da a tun farko aka ce za a ba jama’a naira dubu Takwas da nufin rage radadin cire tallafin mai kuwa sai Dan marayan Zaki ya ce “ai a halin yanzu ma kudin ko naira dari Takwas ba su kai bakasancewar iron yadda abin ya koma a halin yanzu.
” zamu bude shafi ko dai na hagu ko dama, amma hakika za a bude feji wato shafi idan lokacin ya yi”.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.