Home / Labarai / Na Amfana Da Ci Gaban Da Sardauna Ya Kawo – Oshiomhole

Na Amfana Da Ci Gaban Da Sardauna Ya Kawo – Oshiomhole

Mustapha Imrana Abdullahi
Tsohon Gwamnan Jihar Edo kwamared Adam Aliyu Oshiomhole ya bayyana cewa ya na daga cikin mutanen da suka amfana da irin ayyukan da marigayi Sardaunan Sakkwato Sa Ahmadu Bello ya aikata domin ci gaba Nijeriya da kasa baki daya gaba.
Adam Oshiomhole ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da manema labarai jim kadan bayan da ya kammala jawabinsa a wajen babban taron da cibiyar tunawa da Sa Ahmadu Bello da ke Kaduna ta shirya karo na Bakwai.
Adam Oshiomhole ya ci gaba da cewa “hakika ban da irin hangen nesa da marigayi Sardaunan Skkwato ya yi ba da bai zamo abin da ya zama ba a halin yanzu, don haka ni ina daga cikin wadanda suka amfana da kokarin Sa Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato ya aiwatar ba tare da wani ko kwato ba”.
“Shi yasa marigayin Sardauna ya tabbatar da cewa irin Audugar da ake Nomawa a arewacin Nijeriya ba dauke ta aka fitar da ita zuwa Mancasta (manchester) ta kasar Amurka ba, shi ya sa ya ce a kirkiro da masakar Kaduna,wannan Audugar da ake Nomawa daga arewacin Nijeriya a sarrafa ta a nan arewa, masakar Kaduna da aka samar da ita tun a shekarar 1952 na da ma’aikata dubu hudu sai kuma masakar Arewa da suke da ma’aikata akalla dubu hudu ga kuma masakar UNTL da ke da kusan ma’aikata dubu Takwas sai kuma masakar NOSFIN mai ma’aikata akalla dubu uku da su masakar  FINE da dai sauransu, duk wadannan an samar da su ne da nufin karin samar wa jama’a aikin yi domin ingantuwar al’amuran yau da kullum”.
Da nufin samar da aikin yi ga jama’a sannan kuma mutane su zama suna da abin yi a koda yaushe, amma sakamakon tsare  tsaren da ake samu da kuma wasu canje canje shi ne lamarin ya zamo cikin halin da yake ciki a halin yanzu sai masana’antu suka zama babu musamman da Nijeriya ta Sanya hannu a yarjejeniyar WTO wanda hakan ya Sanya kasar a cikin yin gasa da sauran kasashe wanda hakan ya zamarwa kasar matsalar rashin adalci a yanzu, ta yaya wadanda suke tafiyar da masana’antu ta bangare daya kawai za su je su yi gasa da sauran kasashen duniya, alhali baka da wutar lantarki”. Inji shi.
Ya kara da cewa idan aka yi duba da masana’antu a Jihar Kano idan aka yi duba da masana’antun da suke a unguwar Bamfai da suka hada da masana’antar zanin Gano, Dan kamfai, da saura da yawa a unguwar sharada da a kalla su na samar da ma’aikata dubu uku da kuma masana’antun da suke a Zariya da Funtuwa duk wadannan suna yin aiki kuma mutane su na samun abin yi a kullum, kari da masu harkar saye da Sayarwa da suke samun harkar yau da kullum.
Idan ana bukatar samun amfani sosai ba wai za a yi maganar fita da kayan da muke samarwa ba ne, dacewa ya yi a rika sarrafa su ana samar da abubuwan amfanin da za su amfani jama’ar kasa, duk wannan irin abubuwa ne da Sa Ahmadu Bello ya samar daga irin tunaninsa ba wai fadi da baki ba, a’a aiwatar da su a aikace kuma ni ina cikin wadanda suka amfana da wannan.
Idan kuma aka yi batun hadin kan kasa “Ni an haife ni a Jihar Edo ne amma dai ina Kaduna tun a shekarun  16 zuwa 17 ina zaune a Kaduna, na je garin Benin ne na Jihar Edo lokacin da na zama Gwamna ban da haka an zabe ni an kuma an zabe ni ba wanda ya da mu da addini na ko daga ina na fito? Amma dai kowa ya yi imanin zan iya domin lokacin da na zama Janar Sakatare na kungiyar Kwadago na Gona babban ofishin kungiyar da ke Kaduna wanda gagarumin aiki ne kwarai, saboda muna da tsarin cewa masakun Nijeriya za su samar da ma’aikata a kalla miliyan 25, ba tare da sanin cewa lamarin zai juya ba ya zama sama ta koma kasa.
“Ku duba irin yadda aka samu matsala a tsare tsare a Nijeriya, misali irin yadda aka Cefanar da kamfanin da ke rabawa jama’a wutar lantarki na kasa, inda aka Sayarwa da mutanen da ba su san komai ba a lamarin yadda wutar lantarki take, inda kai ne zaka sayi na’urar rarraba wutar lantarki a gidanka amma sai kawai wani mutum ya kawo maka takardar sai ka biya kudin wuta, don haka ina ganin akwai bukatar a tabbatar da koma wa baya game da wadannan irin tsare tsare domin rashin amfaninsu ga yan kasa.
“Ina ganin har yanzu manoma su na kan kokarin Noma Auduga ne, amma idan aka yi duba da irin yadda aka samu nasara a wajen Noman Shinkafa abin farin ciki ne son haka muna ganin lallai ya dace a Farfado da masaku domin a samu ingantar tattalin arzikin kasa, a gaskiya masaku ne rayuwata don haka nake bukatar a Farfado da su saboda ba domin hakan ba idan da tun lokacin da muke aiki duk sun rufe to, wane hali zan kasance?
Saboda haka ko akwai cutar Korona ko ba Korona ya dace a koma samar da kayayyaki daga masana’antu da ta kasance a matsayin babbar hanyar samar da ayyukan yi.

About andiya

Check Also

Group Decries Escalation Of  Insecurity In Birnin Gwari

      By; Our Reporter in Kaduna   The Birnin Gwari Progressive Union(BEPU) has …

Leave a Reply

Your email address will not be published.