Home / News / Na Shirya Gasar Kwallon Kafa Ne Domin Taimakawa Matasa – Abdallah Yusuf

Na Shirya Gasar Kwallon Kafa Ne Domin Taimakawa Matasa – Abdallah Yusuf

Daga Imrana Abdullahi, Kaduna Arewacin Najeriya

Abdallah Yusuf Mamman, matashi ne mai kokarin ganin ya kawo hanyoyin da rayuwar matasa za ta inganta wanda hakan yasa har ya yi tunanin shirya gasar wasan kwallon kafa a tsakanin matasa a Jihar Kaduna.

Kamar yadda matashi Abdallah Yusuf Mamman, ya shaidawa manema labarai cewa ya shirya wannan gasa ne tsakanin kulab din wasan kwallon kafa na matasa guda 16 da suke a cikin garin Kaduna domin karawa matasan kaimin yin abin da ya dace kasancewar matasa ne kashin bayan ci gaba da gina kasa.

“Na yi tunanin shirya wannan gasar ne domin tunawa da wani babban Abokina da ya rasu a kasar Kanada kuma shi babban abokina ne a nan garin Kaduna da ake yin wannan gasar”.

” akwai kulab guda Goma sha shida (16) da an fara yin wannan Gasar kamar yadda aka bude a wannan filin wasa na gidan rediyo da Talbijin na Hamada kuma za a yi ne Kifa daya kwala duk wanda aka zura wa kwallo shikenan an fitar da shi kuma za mu yi wasan karshe ne a sati mai zuwa za a yi wasan karshe da raba kyaututtuka ga dukkan kulab din da ya samu nasarar zama na farko, biyu da na uku da dai abin da ba a rasa ba domin karfafa Gwiwar matasan da suka halarci gasar”.

” Muna da tsarin bayar da kyaututtuka ga wanda ya samu nasarar zama na farko kudi naira dubu dari (100,000) sai na biyu dubu Hamsin (50,000) sai  kulab din da ya zama farko dai sauran kyaututtuka da yawa.

Kuma wani babban lamari shi ne wasan kwallon kafa na taimakawa matasa wajen dauke su daga cikin matsalar zama kawai haka nan na zaman banza, madadin zama haka nan ba abin yi kuma za a rika samun matasa tun suna kanana a same su sun iya wasanni motsa jiki.

Kuma hakan zai taimakawa al’umma domin matasa sun samu abin yi tun suna yan kanana.

“Na kuma lura da wani al’amari a arewacin Najeriya akwai bukatar a samu cibiyoyin horas da matasa wasanni kamar na kwallon kafa wanda hakan ne ya sa nake ganin a irin wannan. Kuma wani babban al’amari ma shi ne na yi tafiye tafiye da dama kasashen duniya don haka sai Naga babu wani amfanin in boye dimbin ilimin da na samu a wasu kasashen duniya don haka nake kokarin in sanarwa da al’umma ta irin abin da na Sani ga horas da matasa”.

Abdallah Yusuf ya ci gaba da bayanin cewa ” matasa masu shekaru a kalla daga sha uku zuwa sha Takwas ne ke da hadarin fadawa cikin wadansu hanyoyi idan ba a yi hattara wajen kulawa da su ba, kamar na shaye shaye da dai sauran wadansu halaye don haka ne wannan zai iya taimaka wa matasan su san ina aka Dosa a rayuwa su amfana har kuma su amfanar da wani ko wasu da dama a cikin al’umma”.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.