Shugaban kungiyar taimakawa manoma na kasa Dokta Aliyu Muhammad Waziri San turakin Tudunwada Kaduna ya bayyana cewa suna tsare tsaren samar da makiyayar Dabbobi a kananan hukumomi dari 774 a tarayyar Najeriya domin Saukakawa makiyaya da kuma dauko hanyar magance matsalar tashe tashen hankula tsakanin manoma da makiyaya.
Dokta Aliyu Muhammad Waziri ya dai bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a Kaduna, inda ya ce hakika kungiyar taimakawa manoma na kokarin daukar matakan yin maganin matsalolin da ke addabar manoma da makiyaya da nufin samar da ci gaban kasa da al’ummarta baki daya.
Kamar yadda shugaban kungiyar NAMCON, Dokta Aliyu Muhammad Waziri ya shaidawa manema labarai cewa wannan matakin wani bangare ne na samar da hanyoyin yin kiwo ma zamani a kasa, da za a iya kara inganta lamarin da kuma yin maganin yawan yin fadace- fadacen da ake yi tsakanin manoma da makiyaya a kasa.
Kamar yadda Dokta Aliyu Waziri Waziri shaidawa manema labarai a Kaduna cewa makiyayar dabbobin ta zamani za a samar mata da ingantaccen abincin Dabbobi mai kyau da inganci, Manya Manyan Dama damai,da dukkan kayan da duniya ke takama da su, wanda hakan zai Sanya makiyaya ba su da wata dama ko hujjar tashi daga wannan wuri zuwa wancan suna yawace yawace suna neman ruwa ko wani abinci da dai jakadancin hakan.
Ya kada da bayanin cewa wannan wurin yin kiwon dabbobin da za a samar zai kunshi wadansu abubuwa kamar dakin shan magani,makarantun Islamiyya da na Boko da sauran abubuwan da ya dace a samu a wurin duk za a yi kokarin samar da su baki daya.
Waziri ya ci gaba da cewa, “wannan wurin kiwo na Dabbobi za a samar masa da duk abin da ya dace da z a iya samun wadatacciyar ciyawar Dabbobi a lokutan rani da Damina suk da nufin samar da wadataccen abinci a kasa, wanda hakan zai taimaka kwarai wajen samar da ayyukan yi da wadataccen abinci tare da rage radadin talauci kuma hakan zai Sanya asusun ajiyar Najeriya a duniya ya ci gaba da habbaka ya na tumbatsa fiye da kuma.
Kamar yadda shugaban na kasa ya bayyana cewa wuraren da za a shuka ciyawar za a samar da wadansu bishiyoyi masu amfani da bunkasa tattalin arzikin kasa da suka hada da Itacen Kashu,Mangoro,Gwaba, da dai sauransu, saboda haka ina tabbatarwa da duniya cewa tsarin zai taimaka wajen yin maganin matsalar fadace fadacen manoma da makiyaya a cikin kasa”, Inji Dokta Aliyu Waziri.
Ya kara da bayanin cewa manufar kungiyar itace bunkasa bangaren Noma ta hanyar yin Noman zamani da taimakawa jama’a ta fuskar yin muhimman tsare tsare.
Ya kuma yi tariyar baya inda ya ce a shekarar 2021 da ta gabata kungiyar NAMCON ta karfafa wa manoma mutane miliyan 15, musamman ma mata da matasa masu kananan shekaru duk a game da harkar Noman zamani.
Sai kuma ya shawarci gwamnati da ta yi amfani da albarkatun da ake samu daga bangaren Noma domin yin maganin matsalar rashin aikin yi da karancin abinci a kasa.