Related Articles
DAGA IMRANA ABDULLAHI
Hadaddiyar kungiyar masu Noman zamani ta kasa (NAMCON) kungiyar da ke kokarin Tallafawa mutasa domin su San dabarun dogaro da kawunansu karkashin jagorancin shugaban kungiyar na kasa Honarabul Dokta Aliyu Muhammad Waziri, dan marayan Zaki, Santurakin Tudun wada Kaduna, Dujuman Buwari kuma hasken matasan Arewa tare da hadin Gwiwar ma’aikatar kula da masana’antu ta Jihar Kano ke farin cikin gayyatar al’ummar kasar Kano baki daya zuwa gagarumin taron yaye dalibai guda dubu 4,572 Maza da Mata da aka Koyar da su dabarun kiwon kaji na zamani domin dogaro da kai.
Za a yi taron ne a ranar Talata 26, ga wannan watan 2022 a filin wasa na Sani Abacha da ke birnin Kano.
Babban bako a wurin taron shi ne Khadimul Islam Gwamnan Jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje. Uban taro San Kano Alhaji Aminu Ado Bayero shugaban taro Danburan Zazzau Alhaji Sani Sha’aban.
Baki na musamman sune Farfesa Yahya Kuta, saga jami’ar Ibadan da Dokta Malami Shehu kwararre kan sha’anin tsaro da Dojta Devid Oyen mai tsara tsimi da tanajin na kungiyar
Sai mai masaukin baki Honarabul Ibrahim Muktar kwamishinan ciniki masana’antu da ma’adinai, ana gayyatar kowa da kowa wannan taro domin shaida horar da matasa sana’o’in dogaro da kai.
Sanarwa daga Abdulhamid Yakubu, ko- odinetan NAMCON reshen Jihar Kano.