Home / News / Osinbajo Bai Ce Zai Samawa ‘ Wakilai 7,000 Masauki A Abuja Ba

Osinbajo Bai Ce Zai Samawa ‘ Wakilai 7,000 Masauki A Abuja Ba

 

From Ibraheem Hamza Muhammad

 

 

Kwamitin Sadarwa na ‘Kungiyar kamfen din neman takarar Shugaban ‘Kasa ta Mataimakin Shugaban ‘Kasa Osinbajo ta ce an yi mata ‘kagen cewa wai zai samawa wakilan Jam’iya 7,000 masaukai a otel-otel a Abuja yayin taron fidda-gwani na Jam’iyar APC.

 

 

Wannan ya biyo bayan ala’kanta labarin ‘karya da akayi na cewa wai Mataimakin Shugaban ‘Kasa Yemi Osinbajo ne ya furta hakan.

Sanarwar da ta fito daga Kwamitin ta ci gaba da cewa, “Mun ga labarin ‘kanzon Kurege da ya ce wai Kwamitin neman zaben Osinbajo ya ce zai samar da dakunan Otel-otel har guda dubu bakwai ( 7000 ) ga wakilai.

 

 

” Zu’ki ta mallen ta ruwaitu cewa, an ala’kanta cewa wai Mai Taimakawa Mataimakin Shugaban ‘Kasa na Musamnan, Sanata Babafemi Ojudu ne wai ya shaidawa wakilan jam’iya haka a Minna, a lokacin da yake zawarcin da a zabi Osinbajo yayin za’ben.”

Sanarwar ta ci gaba da cewa, Sanata Babajide Ojudu bai fadi haka ba, kuma babu wannan shirin na samar da dakuna da abinci ga Wakilai haihata-haihata don ‘karya ce tsagwaronta.

Kwamitin na jaddada cewa, Maigirma Mataimakin Shugaban ‘Kasa yana ci gaba da ganawa da Wakilan Jam’iyar APC da madu ruwa da tsaki a jihohi da amsa tambayoyinsu game da siyasa da jagoranci.

 

 

Sanarwar ta kara da cewa, burin Kwamitin shine na ci gaba da ganawa da ‘Yan jam’iyar APC da burin ganin an tunkuda kasar Najeriya zuwa gaba bayan zaben badi mai zuwa.

 

About andiya

Check Also

PRESIDENT TINUBU COMMENDS DANGOTE GROUP OVER NEW GANTRY PRICE OF DIESEL

  President Bola Tinubu commends the enterprising feat of Dangote Oil and Gas Limited in …

Leave a Reply

Your email address will not be published.