Rage farashin fetur da ‘yan kasuwar man suka yi, ya kasance martani ne kai tsaye ga rage farashin da muka yi a ranar 6 ga watan Nuwamba. Ba sakamakon janye harajin shigo da kayayyakin man fetur na kashi 15% na wucin-gadi ba ne.
Mun rage farashin fetur daga N877 zuwa N828, sannan farashin bakin teku daga N854 zuwa N806.
Mun ci gaba da jajircewa wajen isar da man fetur mai inganci da kuma tabbatar da cewa ‘yan Najeriya sun ci gajiyar tacewa a cikin Najeriya.
THESHIELD Garkuwa