Home / Idon Mikiya / Rarara Ya Kawo Karshen Rigimar Mawakan Kebbi.

Rarara Ya Kawo Karshen Rigimar Mawakan Kebbi.

Fitaccen mawakin siyasar nan Dauda Kahutu Rarara, ya kawo karshen rigimar da ta barke tsakanin wasu mawakan siyasa jihar Kebbi, da kuma wasu daga cikin mukarraban gwamnatin Jihar.
A cikin watan Disamba na shekarar da ta gabata ne, (2019) wata kungiyar mawaka mai suna ”Naff Entertainment” wadanda aka fi sani da “Mawakan APC na Jihar Kebbi” suka saki wata sabuwar wakar su mai suna “Jirgin Yawo”
Wakar ta su, sun yi ta ne akan Siyasar Jihar, sannan kuma ta yi matukar tasiri a cikin Birnin Kebbi, kuma ta yi yawo sosai kamar wuta bazara a lokacin da mawakan suka saketa.
Jihar Kebbi dai tana daya daga cikin jahohin Arewa da wakar Siyasa ta fi kowace tasiri a wurin masu sauraro, akalla gammayar mawaka goma 18 ne suka yi wakar.
Ba a dade da sakin wakar ba, sai aka samu labarin wasu mutane wadanda ba a san ko su wanene ba, sun tare wasu daga cikin mutum 5 da suka yi wakar, sun yi masu bugun kawo wuka, inda aka rika yada hotunan su jina-jina a shafukan Instagram.
Daga cikin mawakan da aka buga, sun hada da, Bello Aljanare, Kabiru A. Sani, Musa Alee, Shamsu Otono, da kuma Ayuba Ibrahim.
Lamarin da yasa har sai da ta kai wasu daga cikin mawaka irin su, Aminu Alan Waka, El-Mu’az Ibrahim Birniwa, da sauran su, sun fito a shafukan su na yanar gizo, sun nuna rashin jin dadin su akan cin mutuncin da aka yi wa ‘yan uwan su mawaka, haka zalika kuma suka bayyana cewa sai sun bi kadin cin mutuncin da aka yi wa mawakan.
Daga nan kuma sai aka rika yada cewar ana neman dukkan mawakan da su ka yi wakar ruwa a jallo, wanda hakan yasa wasu daga cikin su suka yi layar zana aka rasa inda suke.
Ana cikin wannan sa toka-sa-katsi, sai kuma aka samu labarin an gurfanar da wasu daga cikin mawakan 3 cikin wadanda suka yi wakar,  har ma an tura mawakan gidan yari, sakamakon zargin su da cin Mutuncin wasu mutane a cikin wakar.
Mawakan da ake tsare da su sun hada da, Ibrahim S. Fulani, Muhammad Sani, da kuma Musa Na Allah.
Da ya ke yi wa wakilin mu karin bayani game da sabuwar wakar, shugaban kungiyar Mawakan Nafi’u Umar,  ya bayyana cewa wannan waka ta su, ba ta da nasaba da kowa, riga ba wuya ce, domin babu sunan wanda suka kama, kawai dai hannun ka mai sanda ne suka yi, wasu kuma suka tsargu.
Ana cikin haka ne, a jiya Asabar, 11 ga watan Janairu 2020 Fitaccen mawakin siyasar kasar nan Dauda Kahutu Rarara, Takanas ta Kano, ya yi wa Jihar Kebbi dirar Mikiya inda ya gana da Gwamnan Jihar Alhaji Atiku Bagudu a kan lamarin mawakan.
Sai dai Gwamnan ya bayyanawa Rarara dukkan wannan dambarwar da ta faru, bai san ana yi ba. Sannan bai san an yi kara ba, bugu da kari ma baya da masaniya a kan wadanda aka kulle.
Bugudu, ya ci gaba da bayyanawa su Rarara cewa, ai dukkanin Mawakan Jihar Kebbi ‘ya’yan sa ne, sannan idan ma an same su da laifin sun yi masa wani abu wanda bai dace ba ya yafe masu.
A yanzu haka dai ana sa ran idan Allah ya kaimu gobe Litinin za a saki Mawakan da aka kama sakamakon zuwan Rarara.
A cikin mawakan da  suka yi wa Rarara rakiya zuwa Kebbi sun hada da Kamilu Koko, Alhaji Garba Gashuwa da sauran su.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.