Abdullahi Hayin Fago
Wasu kungiyoyin samari karkashin Youth for Peace Initiative (YOPI) sun yi kira ga gwamnatin jihar Kano da ta yi gaggawar girmama umarnin kotun da ta ce sauke Sarkin Kano Aminu Ado Bayero ba a yi shi bisa daidai ba. Sun ce zaman lafiya na tabbata ne yayin da a ke girmama umarnin kotu.
“Kamar yadda umarnin kotu ya ce dawo da Sanusi Lamido Sanusi bisa karagar mulkin Kano ya sabawa doka, saboda haka mu na kira ga gwamnatin jihar Kano da ta yi gaggawar mayar da Aminu Ado Bayero kan karagar mulki ba tare da bata lokaci ba,” in ji matasan.
Kamar yadda shugabannin wadannan kungiyoyi a dunkule daga Masarautun Kano da Gaya da Karaye da Bichi da Rano su ka ambata ta hanyar shugabannin su Salisu Sani da Mustafa Bahago da Muttaqa Labaran da Danjuma Batijjane da Danlami Abdullahi su ka bayyana, su na kira ga Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf da ya yi abinda doka ta tanada.
Su ka ce, “Wai shin ba doka ce ta kawo shi ba ne da gwamnatin tasa? To dan me ya sa zai karbi umarnin kotun da ta kawo shi mulki amma ba zai karbi umarnin kotun da ta ce bai yi daidai ba da ya cire Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero?
Su na mamakin cewa wace irin harka ce haka? Kuma wannan wane irin tunani ne?
Sun yaba da jami’an tsaro a jihar da su ka tsaya ganin cewar an bi umarnin kotu na cewar akwai kuskure wajen dawo da Sanusi Lamido Sanusi a matsayin Sarkin Kano.
Wadannan kungiyoyi sun kara da cewa “Dukkanmu fa mu na son jihar mu ta ci gaba da zaman lafiya yadda a ka san ta. Ba ma son a kai har layin da zai tilasta gwamnatin Tarayya sanya dokar ta baci a jihar.
Saboda haka mu na kira ga Gwamna da gwamnatinsa da lallai lallai su bi doka wajen karbar umarnin kotu.”
Haka nan su ka yi takaicin cewa a dalilin masarautun ne fa a ka kara samun cigaba a wadancan masarautu na Karaye da Gaya da Rano da Bichi.
Amma yanzu, a cewarsu, a na son a mayar da su baya wajen ayyukan raya kasa. Saboda wannan rushewa da a ka yi ba bisa ka’ida ba.