Home / Labarai / Sallar Layya: Shugaban APC Na Zamfara Da Yankin Arewa Maso Yamma, Matawalle Ya Tallafawa Dimbin Al’umma

Sallar Layya: Shugaban APC Na Zamfara Da Yankin Arewa Maso Yamma, Matawalle Ya Tallafawa Dimbin Al’umma

……….Ya Raba Raguna 4,860 da naira miliyan 390 domin jama’a su yi hidimar Sallah Cikin sauki
Sakamakon gabatowar babbar Sallar layya ta shekarar 2024, shugaban jam’iyyar APC na Jihar Zamfara wanda kuma shi ne ministan kasa a ma’aikatar tsaro ta tarayyar Najeriya Dokta Bello Mohammed Matawalle ya rabawa wa jama’a raguna dubu 4,860 domin su samu sukunin yin Sallar cikin walwala da jim dadi.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takardar da ke dauke da sa hannun Yusuf Idris Gusau babban jami’in yada labarai na jam’iyyar APC a Jihar Zamfara.
Tsohon Gwamnan mai taimakon al’umma ya kasance a matsayin wata al’adar da yake yi na taimakon jama’a a kowace shekara ya rabawa jama’a abin da za su yi hidimar Sallah domin a kyautata masu kuma ban da ragunan har ma da karin kudi naira miliyan 390 da wadanda suka amfana za su rarraba ayi cefanen sallah.
Wadandabza su amfanan sun hada da mambobin jam’iyyar APC da kuma sauran jiga Jigan jam’iyyar na jiha da kuma na kananan hukumomi da Mazabu a baki daya na Jihar.
Sauran sun hada da iyayen jam’iyyar da kungiyoyin Maza da mata tare da matasa masu bukata ta musamman, marayu da mabukata da kuma yayan jam’iyyar a Jihar baki daya.
Sauran kuma sun hada da tsifafgin masu rike da mukamai a Gwamnatin matawalle da suka hadada kwamishinoni,masu bayar da shawara, manyan daraktoci, mataimaka na musamman, masu taimakawa Gwamnan,kwamishinonin musamman da jami’an bangarorin gwamnati da dama.
An kuma zabi mutane 140 saga kananan hukumomi 14 na Jihar da aka ba su naira dubu dari dari kowannensu da nufin a taimaka masu su samu kyakkyawan sukunin yin shagalin Sallah.
Da yake nuna farin ciki da irin dimbin goyon bayan da mutanen yankin Arewa maso Yamma ke ba gwamnati da suka yi tururuwa suka zabi shugaba Bola Ahmed Tinubu a lokacin zaben shekarar 2024 da ya gabata wanda kuma a lokacin Matawalle ne babban jami’in kamfe na shugaba Bola Ahmed Tinubu, ministan ya zabo wadansu mutane a yankin inda suma aka yi masu kyauta domin yin shaolin sallah.
Ya kuma yabawa irin gagarumin hadin kai da goyon bayan da suke samu a wannan yankin na Arewa maso Yamma wanda sakamakon hakan ya ce Gwamnatin za ta ci gaba da kokarin ganin an kyautatawa yankin da ayyukan ci gaban da za su amfani al’umma ta yadda za a sharbi romon Dimokuradiyya da kuma kare rayuka da dukiyoyin mama’s baki daya.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.