Home / Labarai / Samar Da Tashar Jirgin Ruwa Ta Funtuwa Ci Gaba Ne – Dangaladima

Samar Da Tashar Jirgin Ruwa Ta Funtuwa Ci Gaba Ne – Dangaladima

Daga Imrana Abdullahi

Kwamandan rundunar hukumar kula da shigi da ficen kayayyaki ta tarayyar Najeriya kwastan na Jihar katsina, S K Dangaladima, ya bayyana tashar Jirgin ruwa ta kan tudu da aka bude a garin Funtuwa a matsayin wani al’amari na ci gaban arewa da kasa baki daya.

S K Dangaladima ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai jim kadan bayan kammala gagarumin taron bude tashar da aka yi a garin Funtuwa inda wakilin shugaban kasa sakataren Gwamnatin tarayyar Najeriya Sanata George Akume, ya bude a madadin shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Dangaladima ya ci gaba da cewa duk kasar da ba ta da kasuwanci hakika tattalin arzikin kasar ba zai motsa ba kuma ya na kawo gagarumin ci gaba idan aka samu hanyoyin kasuwanci masu inganci, kuma wannan zai taimakawa kasashe da dama tun daga nana har kasar Nijar duk kasuwanci zai kara inganta cikin yardar Allah.

Kuma kamar yadda ministan kula da Jiragen ruwa da samar da tattalin arzikin kasa mai inganci ya ce hukumar kwastan su tabbatar komai ya yi wa yan kasuwa sauki hakika za su yi hakan”, inji Dangaladima.

” yanzu haka mutum zai iya zuwa kasashen duniya ya sayo kaya, misali kamar kasar Cina sai mutum idan ya sayo kaya ya rubuta Funtuwa dry port wato tashar Jirgin ruwa ta kan tudu, kayan mutum za su iso nan kai tsaye ba wai sai mutum ya je Legas ya na kashe kudin jirgin sama da na Otal ba, mu kuma kwastan za mu duba mu ga duk abin da ya kasance doka ne za mu yi shi domin al’amura su ta fi cikin sauki”.

Dangaladima, ya kara da bayanin cewa ko a halin yanzu da akwai jami’an hukumar kwastan da suka turo a wannan tashar su rigaya sun zo za su duba wurin domin kamfanin ya rigaya ya samar da wurin da jami’an hukumar za su yi amfani na yanar Gizo, wato kwamfitoci kuma nan da sati daya za a fara yin duk abin da ya dace ayi”.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.