Home / Labarai / Samun Mai Ya Kashe Mana Zuciya Da Arzikin Arewacin Najeriya – Sanata Angoshi

Samun Mai Ya Kashe Mana Zuciya Da Arzikin Arewacin Najeriya – Sanata Angoshi

 

Daga, Bashir Bello, Majalisa Abuja.

Sanata Mohammed Ogoshi Onawo mai wakiltar Nasarawa ta Kudu a majalisar Dattawa ta kasa, ya bayyana cewa samun mai da kuma mayar da hankali a kansa da aka yi ya kashe wa jama’a da yawa zuciya da kuma tattalin arziki.

Sanata Mohammed Ogoshi Onawo, ya bayyana hakan ne  lokacin da yake ganawa da manema labarai a Abuja, a kan batun yadda za a inganta tattalin arzikin Najeriya baki daya ba dole sai an dogara da Man fetur ba.

Ya ci gaba da cewa idan an duba a fannin Noma ya dace a yanzu an bunkasa shi sosai ta yadda a yanzu za a rika yin amfani da Injunan Noma na zamani a rika yin Noma da shi.

“Amma abin mamaki shi ne kowace jiha sai kawai ya zauna a rika jiran me za su samu a wata daga asusun Gwannatin tarayya a dan sammata har lamarin ya kai ga ana kiran yan Arewa da arewacin kasar cima zaune.

Amma a kowace karamar hukuma da muke da ita a cikin dari Bakwai da Saba’in da Bakwai (774) a fadin kasar za a tarar kowace karamar hukuma da akwai ma’adanin da za a iya yin amfani da shi a sarrafa shi a kuma samu abinci da dukkan jama’a, koda yake a halin yanzu tunani na canza wa tunanin duniya na canzawa daga batun Mai saboda a halin da ake ciki a yanzu nan da shekaru Biyar zuwa Goma mai zuwa Mai ba zai iya kawo mana kudin da ake kashewa ba kuma don haka ya dace ayi amfani da wadansu ma’adanan da ke bayar da kudi fiye da Mai domin muna da su shimfide

Hakan ne yasa muka duba Jihohin da suke da ma’adinai da Gwannati za ta ba su dama ta kuma mayar da hankali ta bangaren mai kamar yadda ta mayar da hankali ga Mai aka bunkasa shi, idan an Sanya rabin abin da aka saka a bangaren Mai aka bunkasa shi hakika zai wuce abin da aka samu a bangaren Noma somin akwai albarka kwarai.

Idan an duba, ” giram daya na Kwal nawa ne kuma giram daya na Litiyum nawa ne? Kuma giram daya na Tozali nawa ne duk wadannan fa muna da su, kai Allah na tuba idan kasar da muke da ita ba amfani ko arziki ta yaya mutanen kasar Cina za su zo su Sanya kasar mu a cikin kwantena su kai kasarsu?

A game da batun irin gudunmawar da za su ba Gwamnati a matsayinsu na yan majalisa kuwa sai ya ce idan an duba irin shawarar da mataimakin shugaban kwamitin ya bayar shi ne a duba irin yadda wasu yan kasar Cina ke aiwatar da wadansu abubuwa a nan kasar mu Najeriya wanda idan wani dan Najeriya ya aiwatar da irinsu a can kasar su ta Cina hakika kashe mutum za a yi, saboda haka ne ya dace mu dauki wani matakin da ko bai kai wancan irin nasu ba zai iya tsoratarwa. Na biyu su yan kasar Cina da sauran wadansu mutanen da suka zo nan Najeriya ba kawai da kashin kansu kawai suke zuwa ba suna zuwa Najeriya ne tare da goyon bayan wasu manya na kasa, wanda idan an kama su zaka ga ana ta yawan kiraye kirayen waya kuma zaka ga cewa wanen nan tsohon kaza ne ko tsohon kaza ne.

Wasu ma zaka ga su ne ya dace zu tsare kasar domin ya ci ya koshi amma kuma shi ne ke kokarin haifar da matsala ya na kawo irin wadancan mutane a kasa suna yin abin da ya sabawa dokar kasar da tsare – tsare da dukkan tanaje tanajen da aka yi a kasa.

“Kamar abin da na fadawa minista ne cewa idan an kama wadansu daga cikin yan kasar wajen nan da suka zo idan an yi masu tambaya sun fadi cewa wane ne ya kawo su lallai wasu manyan za su ji kunya su kaucewa irin wannan harka ta kawo yan kasar waje, saboda haka ne muke son hada baki da wannan minista da kuma wannan Gwamnatin domin akwai alamar minista na da kuzari aiwatar da aikin da ya dace a tsarewa kasa da fannin ma’adinai mutunci

Haka zalika Sanata Mohammed Ogoshi Onawo, mai wakiltar mazabar Nasarawa ta Kudu a majalisar Dattawan Najeriya ya yi karin haske game da batun matsalar ruwa da iska da aka samu a watan hudu inda ya ce kawai sai aka tashi aka ga Makarantu, Masallatai,Coci – Coci da shaguna har ma da gidaje aka ga ubangiji ya yi ikonsa kuma ba yadda jama’a za su iya yi domin haka Allah ya Kaddara a kan jama’a ya faru  kuma mafi yawan mutanen da abin nan ya shafe su wadanda ke neman abin da za su ci ne a yau da kullum wasu na fitowa daga Gona ne wasu ma ba abin da za su dauka su sayar kuma muma da Allah ya ba mu dama muna wakiltar su ba mu da abin da zai ishe su da har za mu ba su domin su gyara gidaje ko wuraren neman abincinsu, abin mamaki ma har gidaje wadansu duk sun rushe.

Hakan ne ta Sanya muka kawo kuka ga majalisa da nufin Gwannatin tarayya ta kawo dauki gare su akwai hukumomin da aka kafa su musamman domin yin irin wannan hakan ya sa muka rubuta wasika muka kai masu, amma domin duniya ta Sani cewa ni a matsayina na wakilinsu na damu da wannan domin ni wakilinsu ne a majalisa shi yasa na kawo kuka ga majalisa.

Kamar yadda kun ji dan uwana ya fadi, majalisa za ta tattauna ta kuma cimma matsaya sannan a aikawa wadannan hukumomin domin su aiwatar da aikin, akwai kuma kwamiti a majalisa da aikinsu shi ne su bi domin ganin ko an aiwatar da abin da aka ce ayi bayan cimma yarjejeniyar abin da za a yi. Hakan ya sa na samu shugaban kwamitin komai da ruwanka na majalisar Dattawan wanda hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa ( NEMA) na karkashinta ne shugaban kwamitin ya kuma tabbatar Mani cewa har ya yi magana da shugaban hukuma kuma har an fara daukar mataki.

A game da ko suna da kiyasin yawan irin asarar da aka yi ta gidaje, Gonaki shaguna da dai sauran abin da ya lalace, sai Sanata Ogoshi ya kada baki ya ce to, mu dai mun san wannan lamari ya shafi kananan hukumomi Uku ne don haka za a iya cewa fiye da dari abin ya shafa kuma dalilin da yasa na ce ba zan iya kiyastawa ba shi ne a halin yanzu ana cikin wani yanayi na hauhawar farashi don haka idan an yi lisaafin kudi kaza ko kaza ana iya komawa wurin da aka taya kayan a tarar farashin ya tashi, saboda haka mutane sun yi asara mai dimbin yawa kuma muna kyautata zaton cewa Gwamnati za ta iya kimantawa da abin da za ta iya taimakawa domin Allah ya yi mu kuma bukatun mu suna da yawa don haka biyan bukatun nan sai shi Allah kawai

About andiya

Check Also

Dalilin Zuwan MACBAN Majalisar Wakilai  Shi Ne – Ibrahim Almustapha

Bashir Bello Majalisar Abuja Dan majalisar wakilan Najeriya  Honarabul Ibrahim Mustapha Aliyu, shugaban kwamitin alternate …

Leave a Reply

Your email address will not be published.