Sakamakon irin Nagarta da kokarin aiwatar da ayyuka domin ci gaban jama’ a yasa ake yi wa tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato da ya yi Gwamna tsawon shekaru Takwas tare da gudanar da dimbin ayyukan raya kasa a birni da karkarar Jihar Sakkwato da nufin inganta rayuwar jama’a.
Kamar yadda aka Sani dai Sanata Aminu waziri Tambuwal sananne ne da ya fice wajen yin aiki tukuru domin tarayyar Najeriya da nahiyar Afrika ta ci gaba, musamman kasancewarsa mutumin da ya zama kakakin majalisar wakilai ta kasa da ya yi bayar da kyakkyawan shugabanci da ya zama abin yin koyi ga kowa.
Saboda irin wannan Nagarta da Sanata Amini Waziri Tambuwal keda ita da duniya ta shaida hakan ya sa mutane masu kokarin ganin rayuwar jama’a ta inganta a kowane fanni na rayuwa, Honarabul Atiku Muhammad Yabo, yake tsaye kai da fata sai wajen goyon baya da kuma nuna tarayya hadi da biyayya ga Sanata Aminu Waziri Tmbuwal da nufin a gudu tare a tsira tare.
Sabanin irin yadda Sanata Aminu Waziri Tambuwal a lokacin da ya na Gwamnan Jihar Sakkwato, ya taba yin korafin cewa baya samun kururantawa daga bangaren yan jarida duk da irin dimbin ayyukan da yake aiwatarwa a birni da karkatar Jihar Sakkwato domin inganta rayuwar jama’a.
Hakan yasa a halin yanzu Honarabul Atiku Muhammad Yabo, yake daukar nauyin yi wa duniya cikakke kuma ingantaccen sahihin bayanin ayyukan da Aminu Waziri Tambuwal ya aiwatar tun a lokacin da ya na Gwamnan Jihar Sakkwato wanda mutane a cikin Najeriya da wadansu kasashen Ketare ke tattaunawa a kai sakamakon irin yadda suke karanta dimbin ayyukan da Aminu Tambuwal, ya aiwatar a lokacin ya na Gwamnan Jihar Sakkwato, kuma wannan aikin fadakarwa tare da yayata ayyukan Honarabul Atiku Muhammad Yabo ne ke daukar nauyin hakan.
Abin da duk Honarabul Atiku Muhammad Yabo, ke fadi da kuma a rubuce ana yi ne tare da sunan aikin da aka yi da kuma a wuraren da aka aiwatar da aikin a fayyace suk domin duniya ta fadaka ta kuma amfana da abin da jajirtaccen shugaba ya aiwatar domin amfanin jama’a.
Kuma za a iya cewa Allah ya yi wa jama’ar Jihar Sakkwato, arewqcin Najeriya da kasa baki daya gyadar Dogo sakamakon samun jigo kuma jagora masanin makamar aiki da ya san aikin majalisa da a yanzu aka samu Sanata Aminu Waziri Tambuwal a matsayin zababben Sanata daga Jihar Sakkwato da a halin yanzu aka kaddamar da majalisa ta Goma (10) rare da shi a matsayin Sanata.
Ayyukan da Honarabul Atiku Muhammad Yabo, ke yayatawa sun hada da wadanda aka yi a fannonin samar da kiwon lafiya, bunkasa harkokin Noma, Samar da ruwan sha, bunkasa ilimi,samar da ingantattun hanyoyi a birni da karkara, Samar da ingantaccen hasken wutar lantarki da dai sauran dimbin ayyukan alkairi da Sanata Aminu Waziri Tambuwal ya aiwatar wanda a nan gaba zamu ci gaba da kawo maku wuraren da aka aiwatar da aikin dalla dalla da nufin a rarrabe tsakanin Aya da tsakuwa.
Za a iya cewa majalisar Dattawa ta samu masu aiwatar da aiki tukuru a cikin ilimi da basira.